Muhimman Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani Game da Nnamdi Kanu Shugaban IPOB

Muhimman Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani Game da Nnamdi Kanu Shugaban IPOB

A yau ne rahotanni suka bayyana cewa, an kame shugaban kungiyar tsageru masu fafutukar ballewa daga Najeriya na IPOB, Nnamdi Kanu.

Masu bibiyar Legit.ng Hausa za su so sanin wanene wannan Nnamdi Kanu da aka kame har ake ta cece-kuce akansa.

Wannan yasa, muka tattaro bayanai masu muhimmanci game da Nnamdi Kanu domin mai karatu ya san wanene shugaban na IPOB.

1. Sunansa da asalinsa

Sunansa Nwannekaenyi Nnamdi Okwu Kanu, an haife shi 25 ga Satumba 1967 a Isiama Afara ta jihar Abia, Najeriya kuma yana da takardar zama dan kasa a Burtaniya, jaridar Sun ta tattaro.

Ya yi karatu a jami'ar Najeriya ta Nsukka. Ya bayyana a wani hira cewa, shi mabiyin addinin Yahudunci ne, in ji Forward.

KARANTA WANNAN: Tsadar Abinci: CBN Ta Gano Mafita Kan Tsadar Masara, Za Ta Tallafawa 'Yan Kasa

Muhimman Abubuwa X da Ya Kamata Ku Sani Game da Nnamdi Kanu da Aka Kame
Lokacin da aka kame Nnamdi Kanu | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

2. Ayyukansa

Nnamdi Kanu ya kasance mai fafutukar kafa haramtacciyar Biafra wacce ake cece-kuce akai. Ya bude gidan rediyo a shekarar 2009 don yada manufofinsa na kebe al'ummar Biafra daga Najeriya, BBC ta tattaro.

3. Umarnin daukar makami

A watan Disambar 2020, Kanu ya sanar da kafa kungiyar tsaro ta Gabas (ESN), rundunar tsaro ta yankin Biafra tare da sanar da cewa za su dauki makami, The Nation ta ruwaito.

Daga baya Kanu ya ba dukkan gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya kwanaki 14 don hana kiwo a fili, inda ya yi barazanar tura kungiyar ta ESN don aiwatar da dokar idan hukuma ba ta yi hakan ba.

4. Kameshi

A ranar 18 ga Oktoba 15, 2015, an ba da rahoton 'yan sandan farin kaya na DSS sun kama Kanu a Jihar Legas.

A ranar 19 ga Oktoba, 2015, aka ruwaito cewa an ba da belin Nnamdi Kanu bayan gabatar da shi a asirce a Kotun Majistare dake Wuse 11, in ji jaridar Vanguard.

Daga karshe an gurfanar da Kanu a ranar 23 ga Nuwamba, 2015 a wata Kotun Majistare da ke Abuja a karon farko bisa tuhumar "kitsa aikata laifi, tursasawa da zama memba na wata haramtacciyar kungiya" daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya (DSS).

5. Sako shi daga magarkama

Bayan sanar da ba da belin Kanu, duk da haka, kafofin watsa labarai da ke goyon bayan manufofin IPOB sun kira belin "mai rikitarwa" kuma sun yi ikirarin cewa DSS ta ba da sanarwar belin ne kawai "don huce fushin mutanen Biafra".

Daga karshe Mai Shari’a Binta Nyako ta bada belin Kanu saboda dalilai na rashin lafiya.

6. Abubuwa masu rikitarwa game Nnamdi Kanu

Wani lokaci a 2017, an saki bidiyon Kanu inda ya ke barazanar kisa ga tsohon shugaban Najeriya Obasanjo. Ya fada wa taron magoya bayansa a gidansa cewa idan wani abu ya same shi, mambobin IPOB su hallaka Obasanjo da nasabarsa, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Maganar ta Kanu martani ne ga maganar Obasanjo a wani taro da aka yi a Abuja cewa dole ne ayi mai yiwuwa don dakatar da IPOB.

A watan Afrilu na shekarar 2020, 'yar jaridar nan mai binciken kwakwaf a Najeriya, Kemi Omololu-Olunloyo ta yi ikirarin cewa Nnamdi Kanu ya mutu.

Bayan haka, a ranar 7 ga Maris, 2020, Daily Post ta ruwaito cewa kungiyoyin Arewa da na Kudanci, Peace Accord Forum (PAF) sun yi imani Nnamdi Kanu ya mutu.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

Yanzu-Yanzu: An kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB, an dawo da shi Nigeria

A wani labarin, An kama shugaban kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Amma News Wire ta ruwaito cewa ministan shari'a kuma Attoni Janar, Abubakar Malami ya tabbatarwa da hakan yana mai cewa an kama shi ne ranar Lahadi 27 ga watan Yuni kuma an dawo da shi Nigeria ya fuskanci shari'a.

Ya ce an kama shi ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron Nigeria da yan sandan kasa da kasa Interpol.

Malami ya kara da cewa za a gurfanar da Kanu a gaban alkali a babban kotun tarayya Abuja domin cigaba da shari'a da ake masa na tuhumar laifuka da suka shafi cin amanar kasa, mallakar bindiga ba tare da ka'ida ba da kafa kungiya ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel