PDP ta kira taron gaggawa bayan wani gwamna na kokarin komawa APC

PDP ta kira taron gaggawa bayan wani gwamna na kokarin komawa APC

  • Kwamitin ayyuka na PDP ya kira taron gaggawa a yau Litinin kan batun tserewar Matawalle zuwa APC
  • Kamar yadda Kola Ologbondiyan ya sanar, taron na gaggawa ne kuma hankali ya daga bayan jin cewa gwamnan Zamfara zai musu tawaye
  • Duk da sanar da shirin sauya shekarsa da yake, PDP tace bai sanar da ita cewa zai koma jam'iyyar APC ba

Kwamitin ayyuka na jami'yyar PDP ya kira taron gaggawa a yau Litinin domin tattaunawa kan sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle zai yi zuwa jam'iyyar APC.

Kamar yadda ThisDay ta ruwaito, a wani sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya fitar, ya ce suna gayyatar gwamnoni masu goyon baya don su halarci sauya shekar.

KU KARANTA: Ganduje na kokarin tsige Rimingado saboda bincikar iyalansa da yake kan wasu kwangiloli

PDP ta kira taron gaggawa bayan wani gwamna na kokarin komawa APC
PDP ta kira taron gaggawa bayan wani gwamna na kokarin komawa APC. Hoto daga thisdaylive.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kungiyar Niger Delta Avengers ta dawo, ta sha alwashin gurgunta tattalin arzikin Najeriya

Takardar ta kara da cewa, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje tare da wasu jiga-jigan APC zasu karba gwamnan jihar Zamfaran.

Darakta janar na yada labarai na jihar, Idris Yusuf, ya sanar da ThisDay cewa gwamnan zai yi jawabi ga manema labarai kan hakan a gobe.

Amma a ranar Litinin, PDP ta ce Matawalle bai sanar da jam'iyyar cewa zai sauya sheka zuwa APC ba.

Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce: "Abinda kawai zan iya ce muku shine za a yi taron gaggawa na jam'iyyar a ranar Litinin kuma za a tattauna kan rahoton sauya sheka.

"Har a yanzu gwamnan bai sanar da PDP cewa zai bar jam'iyyar ba."

Amma kuma batutuwan dake tasowa na nuna cewa bai zai yuwu Matawalle ya bar jam'iyyar PDP ba bisa shari'a ba.

Dalilin kuwa shine hukuncin kotun koli wanda ta bukaci a mika ragamar mulkin jihar Zamfara hannun PDP bayan zaben 2019, sannan kuma bata duba wani ba, jam'iyyar PDP kadai ta duba.

Hukuncin kotun kolin ya nuna cewa PDP ce ke da kujerar gwamnan jihar Zamfara ba wai Matawalle ba.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bada umarnin dakatar da wata kungiyar taimako ta kasar waje mai suna ACTED bayan bankado cewa suna koyar da jama'a harbi a wani otal dake Maiduguri.

Mai magana da yawun Zulum, Isa Gusau, ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook inda ya sanar da umarnin gwamnan tare da cewa kungiyar ta asalin Faransa an kamata ne da bindigogin wasa kuma tana koyar da harbi a Maiduguri.

Gusau yayi bayanin cewa mazauna kusa da otal din sun kaiwa jami'ai rahoton cewa suna jin harbin bindiga daga otal, lamarin da yasa jami'an gwamnati suka kai kara ofishin 'yan sandan har aka tattaro aka zo duba otal din.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel