Karin kudin makaranta: Kaduna ta musanta amfani da jami'an tsaro wurin muzgunawa dalibai

Karin kudin makaranta: Kaduna ta musanta amfani da jami'an tsaro wurin muzgunawa dalibai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya musanta amfani da jami'an tsaro wurin musgunawa dalibai masu zanga-zanga
  • Malam Nasiru ya sanar da hakan ne ta bakin kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan
  • Gwamnan ya ce yanzu haka yana jiran rahotannin sojoji, 'yan sanda, DSS, hukumar makarantar da sarakunan gargajiyan yankin

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahoto dake yawo na cewa ta tura jami'an tsaro domin musgunawa dalibai masu zanga-zanga a kwalejin ilimi, wanda hakan ya janyo ajalin dalibi daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan yana zuwa ne bayan sa'o'i kadan da jami'an tsaro suka harbe wani dalibi daga cikin daruruwan dake zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

KU KARANTA: Kwamandojin Boko Haram da ISWAP na taro, NAF sun yi luguden wuta a yankin tafkin Chadi

Karin kudin makaranta: Kaduna ta musanta amfani da jami'an tsaro wurin muzgunawa dalibai
Karin kudin makaranta: Kaduna ta musanta amfani da jami'an tsaro wurin muzgunawa dalibai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama jami'in dake karbar rashawa da bukatar kwanciya da masu laifi

A wani bayani ga manema labarai da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan yayi, ya ce gwamnatin jihar Kaduna tana jiran bayanai domin su bata damar gano abinda ke kunshe a cikin rikicin da ya barke a Gidan Waya.

"A binciken farko da aka samu, dalibi daya ya rasa ransa yayin da wasu suka samu miyagun raunika yayin da jami'an tsaro uku suka jigata," yace.

“A lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnan yana jiran rahotanni daga sojoji, 'yan sanda, DSS, hukumar makarantar, kungiyar dalibai tare da sauran sarakunan gargajiya dake yankin.

"Gwamnati za ta sanar da abinda ta samu na rahoto," takardar tace.

Kungiyar daliban Najeriya ta kasa tace za ta mayar da gagarumin taronta na kasa jihar Kaduna kuma za ta yi zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce ba zai yi kasa a guiwa ba wurin ba kowanne bafulatani fili in har yayi niyyar kiwon shanunsa amma a killace.

A yayin jawabi a Abuja a bikin cikar Farfesa Iyorwuese Hagher shekaru 72 a duniya, Ortom ya musanta ikirarin da ake na cewa yana fada da Fulani, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce tarihi ya nuna cewa jama'ar jihar na da alaka mai kyau da Fulani. Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta soki dokar hana kiwo a fili ba inda tace kiwo a killace yafi komai amfani.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel