'Yan majalisar Zamfara baki ɗayansu za su bi Matawalle zuwa jam'iyyar APC, Hadimin Gwamna

'Yan majalisar Zamfara baki ɗayansu za su bi Matawalle zuwa jam'iyyar APC, Hadimin Gwamna

  • Gwamnan Zamfara,Bello Matawalle zai koma jam'iyyar APC tare da manyan kusoshin gwamnati
  • Matawalle, wanda duk gwamnonin APC zasu halarci bikin karbar sa zai koma tare da yan majalisar jihar da na tarayya
  • Mai magana da yawun gwamnan ne ya bayyana haka, tare da shaida cewa dama akwai kyakkyawar alaka tsakanin.gwamnan da jam'iyyun adawa

Bello Matawalle, gwamnan Zamfara, ya shirya tsaf don chanja sheka zuwa jam'iyyar All Progreesives Congress, APC, ranar Talata, The Cable ta ruwaito.

The Cable ta ruwaito cewa Yusuf Idris, mai magana da yawun gwamnan, ya ce gwamnan zai koma babbar jam'iyyar hamayya tare da yan majalisar jiha da na tarayya da kuma duk mukarraban PDP a matakin jiha.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

Gwamnan, wanda aka zaba karkashin inuwar PDP, ya sauke gaba daya mukarrabansa, a wani yunkuri na chanjin shekar.

"Yanzu komai ya kankama ga gwamnan mu don ficewa daga PDP zuwa APC," kamar yadda Idris ya bayyana ranar Lahadi.
"Dukkanin kwamitocin da aka kirkira don tabbatar da tarbar gwamnan sun bayyana yadda shiri ya kankama na bikin tarbar gwamnan a Gusau ranar Talata, 29 ga watan Yuni
"Bari na shaida mu ku cewa dama yan siyasar Zamfara tsintsiya ce madauri daya kuma ko da yake gwamna a PDP, mai gidana, Gwamna Bello Matawalle yayi hulda mai kyau da yan jam'iyyun adawa.

KU KARANTA: Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

"Mutane da dama daga ko wanne bangare sun bi gwamna don bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar, wasu a cikin irin wadannan mutane sun rike manyan mukamai kuma sunyi kokari matuka.
"A wannan komawar APC, wanda gwamnoni 18 na APC zasu halarta, gwamnan zai tafi tare da yan majalisar jiha da na tarayya da kuma duk mukarraban sa a kowane mataki na jihar."

Ya kuma kara da cewa mai gidan nasa zai samu tarba daga Mai Mala Buni, gwamnan Yobe, kuma shugaban rikon kwarya na APC.

Ku tashi ku kare kanku daga 'yan bindiga, Matawalle

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164