Gwamnatin Kaduna ta yi magana kan zanga-zangar da ɗalibai suka yi a Kwalejin Gidan Waya
- Gwamnatin jihar Kano ta ce tana jiran rahotanni daga sojoji, yan sanda, DSS, kungiyar dalibai da wasu kafin yin tsokaci kan lamarin
- Gwamnatin na Kaduna ta kuma ce rahotannin da ke cewa ta tura jami'an tsaro su hana a yi zanga-zangar ba gaskiya bane
- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan dalibin da ya rasu ya kuma yi wa wadanda jikkata fatan samun sauki
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana jiran cikaken rahoto a kan zanga-zangar da daliban Kwallejin Ilimi na Gwamnatin Kaduna da ke Gidan Waya suka yi.
Sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Litinin ya ce a halin yanzu rahoton da gwamnati ta samu shine dalibi daya ya rasu, wasu sun jikkata sannan jami'an tsaro uku sun samu rauni.
DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Zamfara baki ɗayansu za su bi Matawalle zuwa jam'iyyar APC, Hadimin Gwamna
Gwamnati ba ta tura jami'an tsaro su hana zanga-zanga ba
Har wa yau gwamnatin na jihar Kaduna ta ce bata tura jami'an tsaro domin su hana zanga-zangar ko musgunawa daliban da ke yin ta ba.
Gwamnatin jihar Kadunan ta kuma karyata rahotannin da ke cewa ta tura jami'an tsaro su musgunawa masu yin zanga-zangar.
KU KARANTA: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano
Aruwan ya ce:
"Gwamnatin jihar Kaduna na jiran rahoto domin ta fahimci abin da ya haifar da rikicin da ya faru a Gidan Waya.
"A lokacin fitar da wannan sanarwar, Gwamna na jiran rahoto daga sojoji, yan sanda, DSS da mahukunta a makarantar, kungiyar dalibai da kuma masu sarautun gargajiya a yankin."
Ya kara da cewa gwamnatin za ta bayyana abin da ta gano bayan samun cikaken rahoton.
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan dalibin da ya rasa ransa yana kuma yi wa sauran daliban da jami'an tsaro fatan samun sauki cikin gaggawa.
A baya, mun kawo muku cewa an bindige dalibin kwallejin Iimi na Gidan Waya da ke karamar hukumar Jema'a a jihar Kaduna har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Marigayin yana zanga-zanga ne tare da yan uwansa dalibai da suka fito domin nuna rashin amincewarsu da karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi a baya bayan nan, amma sai jami'an tsaro suka zo suna kokarin tarwatsa su.
Wani daya daga cikin masu zanga-zangar da ya yi magana da Daily Trust amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun fito ne su nuna kin amincewarsu da karin kudin makaranta da aka yi kawai sai suka hadu da jami'an tsaron a waje.
Asali: Legit.ng