Bayan Harbe Mata Mai Juna Biyu da Sace Mijinta, 'Yan Bindiga Sun Nemi Fansa N3Om

Bayan Harbe Mata Mai Juna Biyu da Sace Mijinta, 'Yan Bindiga Sun Nemi Fansa N3Om

  • 'Yan bindiga sun sace wani mazauni Offa, sun kuma harbe matarsa har lahira kafin su yi awon gaba dashi
  • Sun bayyana cewa, dole ne iyalansa su tara Naira miliyan 30 kafin su amince su sako mutumin
  • Iyalan sun ce uni sun fara tara kudin, sun ba da miliyan biyu wanda 'yan bindigan suka ki karba

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wata mata mai juna biyu a jihar Kwara sun nemi a ba su kudin fansa na Naira miliyan 30 ga mijinta da suka sace, The Nation ta ruwaito.

‘Yan bindigar sun harbe matar mai juna har lahira sannan suka yi garkuwa da mijinta a ranar Asabar din da ta gabata a Offa, cikin karamar hukumar Offa ta jihar Kwara.

Wata majiya daga dangin wadanda masifar ta rutsa dasu ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, inda ta ce sun sami damar tara Naira miliyan biyu.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Fasinjoji Sun Makale a Daji Bayan da Jirgin Kasa Ya Lalace a Kaduna

Bayan Harbe Mata Mai Juna Biyu Tare da Sace Mijinta, 'Yan Bindiga Sun Nemi Fansar N3Om
'Yan Bindiga Dauke da Makamai | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Majiyar ta ce:

“Sun nemi iyalin su biya Naira miliyan 30 kudin fansa kafin mu samu a sako shi. Amma mun sami damar tara Naira miliyan biyu ne kawai wanda suka ki karba.
"Mun riga mun rasa uwa mai juna biyu, Hawa wacce harsashi ya buge ta lokacin da masu garkuwar ke harbi ba kakkautawa yayin barnar."

'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

Wasu ‘yan bindiga, a ranar Asabar, sun harbe wata mata mai ciki har lahira tare da yin garkuwa da mijinta a karamar hukumar Offa da ke Jihar Kwara.

Marigayiyar, wacce wasu majiyoyi suka bayyana sunanta da Hawa, matar Lukman Ibrahim, wani dillalin wayar salula a Kasuwar Owode wanda aka fi sani da "LUKTECH", Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin, ya faru ne a daren Asabar 'yan mintoci kadan kafin karfe 7 na yamma yayin da Lukman ke tuka surukinsa, matarsa ​​mai juna biyu da yaronsu zuwa gida a kan hanyar Ojoku, kusa da Hedikwatar 'yan sanda

KU KARANTA: PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai ga ’Yan Bindiga

A wani labarin, Wani Sufeton ‘yan sanda, Nathaniel Manasseh, ya shiga hannun 'yan sanda a Jihar Kuros Riba bisa zargin dillancin bindigogi da alburusai ga masu aikata laifuka.

An cafke Manasseh a Calabar, babban birnin jihar, kuma aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda ranar Talata tare da sauran wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, an ce shi babban dillalin bindiga ne kuma ya dade yana wannan harkallar kafin dubunsa ya cika.

Sufeton da ya amsa laifin shi, an ce shi ne ke kula da ma'ajiyar makamai a rundunar 'yan sanda ta jihar kuma an kama shi ne lokacin da ya kasa ba da bahasin wasu kayan aiki ciki har da bindigogin AK-47 guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel