Tsohon shugaba Jonathan ya magantu kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

Tsohon shugaba Jonathan ya magantu kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya ya magantu kan abubuwan da ke jawo ta'addanci a Najeriya
  • A cewarsa, yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi ne ya jefa Najeriya zuwa halin da take ciki
  • Ya kuma koka kan yadda kungiyoyin asiri suka yawaita a tsakanin daliban sakandare da na firamare

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan karuwar aikata laifuka a kasar yana mai cewa galibinsu shan miyagun kwayoyi ne ke jawo su.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi tir da bayyanar kungiyoyin asiri a makarantun sakandare da firamare

A cewarsa, wannan ba karamin abin takaici bane saboda ya kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTRA: Yanzun nan: Gwamnoni sun isa fadar sarkin Kano da nufin tsara bikin Yusuf Buhari

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya magantu kan abubuwan da ke ingiza ta'addanci
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jonathan yace:

"Yanzu muna da kungiyoyin asiri a makarantun firamare da sakandare, a baya ya tsaya a manyan makarantu, amma yanzu zaku ga yara a wadannan makarantun suna tunanin yadda za su kashe sa'anninsu, wannan abin bakin ciki ne."

Da yake halartar taro ta yanar gizo a ranar Juma'a, Jonathan ya kara da cewa matsalolin tabin hankali sun zama kalubale kasancewar mafi yawan 'yan Najeriya suna cikin halin damuwa da abubuwan da ke faruwa a cikin al'umma.

“Mafi yawan wadannan laifuffukan da aka tabbatar, shan kwayoyi ne suka haifar da su, saboda babu wani dan Najeriya mai hankali da zai je ya aikata laifi sai dai idan yana cikin mayen wani abu.
“Ka yi tunanin farkawa da labarin kisan kai da safe, zai bar ka da tunani a zuciyar ka. Har ila yau, ya kamata mu kuma bincika batun lafiyar kwakwalwa."

Barnar Boko Haram da Na 'Yan Bindiga Basu Kai Illar Shan Miyagun Kwayoyi Ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa fataucin miyagun kwayoyi ya haifar da manyan hadurra ga Najeriya fiye da ayyukan 'yan ta'adda mabambanta.

Shugaban na Najeriya ya yi wannan bayani ne a ranar 26 ga Yuni, a yayin kaddamar da shirin yaki da miyagun kwayoyi na WADA, The Nation ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce yaki da shan miyagun kwayoyi yaki ne da dole ne a yi shi ba kakkautawa.

KU KARANTA: Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba

Kamar Yadda Gwajin HIV Yake Dole Kafin Aure, Haka Ma Na Shan Kwayoyi, Buba Marwa

A wani labarin, Janar Buba Marwa (mai ritaya), shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ya bayyana bukatar gwajin shan miyagun kwayoyi kafin a yi aure kamar yadda ake na HIV.

Buba Marwa ya fadi hakan ne a wata hira da BBC Hausa albarkacin ranar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyo Ta Duniya da ake yi duk ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara.

Yayin da yake zantawa, Marwa ya ce:

"A kasar nan, mutum daya cikin bakwai, yana shaye-shaye. Majalisar dinkin duniya a kowace shekara tana zaban rana daya, wanda duniya za ta hade a yi jawabi kuma a nemi mafita game da shaye-shaye a duniya baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel