Da duminsa: Kungiyar Niger Delta Avengers ta dawo, ta sha alwashin gurgunta tattalin arzikin Najeriya

Da duminsa: Kungiyar Niger Delta Avengers ta dawo, ta sha alwashin gurgunta tattalin arzikin Najeriya

  • Tsagerun yankin Niger Delta wadanda ake kira da Avengers sun sha alwashin dawowa da miyagun ayyukansu
  • Kamar yadda suka bayyana, babu shakka sai sun gurgunta tattalin arzikin kasar nan a wannan karon
  • Tsagerun sun kara da shan alwashin cewa zasu ga bayan duk wani dan siyasa mai taimakawa FG wurin durkusar da yankinsu

Kungiyar tsageru ta Niger Delta Avengers, wacce aka sani da tada kayar baya a yankin Niger Delta yayin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na farko, sun sanar da dawowarsu, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Idan za a tuna, kungiyar ta gurgunta tattalin arzikin Najeriya daga 2016 zuwa 2018 ta hanyar kai farmaki wuraren diban man fetur dake yankin, lamarin da yasa kasar Najeriya ta fada karayar tattalin arziki.

KU KARANTA: Acuci maza: Hoton tsohuwa mai shekaru 75 ta koma tsuleliyar budurwa ya janyo cece-kuce

Da duminsa: Kungiyar Niger Delta Avengers ta dawo, ta sha alwashin gurgunta tattalin arzikin Najeriya
Da duminsa: Kungiyar Niger Delta Avengers ta dawo, ta sha alwashin gurgunta tattalin arzikin Najeriya. Hoto daga withinnigeria.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin Borno ta dauka mataki kan dakatar da dalibai saboda basu tari Buhari ba

A wata takarda da suka baiwa manema labarai a ranar Asabar, kungiyar tsagerun ta ce ta kaddamar da 'Operation Humble' wanda take son amfani dashi wurin gurgunta tattalin arzikin kasar nan kamar yadda tayi a baya.

Kamar yadda takardar tace, kungiyar ta sha alwashin ganin bayan 'yan siyasa masu aiki da gwamnatin tarayya wurin durkusar da yankin Neja Delta, Within Nigeria ta ruwaito.

"Abun takaici ne yadda duk da yankinmu ya zama jigo a tattalin arziki kuma muka bada hadin kai wurin kwasar man fetur a yankin, wanda dashi ake amfani a kasar nan, yankin Neja Delta da kudu-kudu ya zama mafi rashin cigaba a kasar nan," takardar tace.

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya ce shiga daji da yake yi domin tattaunawa da 'yan bindiga duk yana yi ne da hadin guiwar hukumomin gwamnati da cibiyoyin tsaro.

Gumi ya tabbatar da cewa bai taba yin wani laifi ba in dai batun shiga daji ne domin tattaunawa da 'yan bindiga, Channels TV ta ruwaito.

Ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni bayan kammala sallar Juma'a a masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng