APC ta dawo kamar yadda take da, Buhari yace rikicin jam'iyya ya kare

APC ta dawo kamar yadda take da, Buhari yace rikicin jam'iyya ya kare

  • Shugaba Buhari yace jam'iyyar APC ta murmure kuma ta dawo da karfinta kamar a baya
  • Shugaban yace da farko tsabar rashin zaman lafiya ya samu wuri ya zauna a jam'iyyar
  • Buhari ya ce wayar da kai da aka dinga yi da aikin 'yan kwamitin ya haifar da ababen amfani ga jam'iyyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce jam'iyyar APC ta dawo kamar yadda take kuma ta tsallake dukkan matsalolin dake cikin jam'iyyar.

Shugaban kasar ya ce jam'iyyar ta farfado, cike da karfinta kuma ta gyara komai na cikin gida domin zabukanta na gaba, The Cable ta ruwaito.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Juma'a a wani taron da yayi da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda ke samun shugabancin Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe.

KU KARANTA: Biloniyoyi 5 a Najeriya da jimillar dukiyarsu za ta iya fitar da kowa a kasar daga fatara

APC ta dawo kamar yadda take da, Buhari yace rikicin jam'iyya ya kare
APC ta dawo kamar yadda take da, Buhari yace rikicin jam'iyya ya kare. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Facebook

KU KARANTA: Acuci maza: Hoton tsohuwa mai shekaru 75 ta koma tsuleliyar budurwa ya janyo cece-kuce

Ya ce: "Cike da zakuwa na saurari irin ayyuka tukuru da kuka yi zuwa yanzu. Kowannenmu shaida ne kan rikicin da ya hadiye jam'iyyarmu wanda ya kai ga shari'a da kuma bayyana son kai da rabuwar kai."

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Buni wanda shine shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, ya ce kwamitin ya tunkari aikin da jajircewa tare da sadaukarwa na ganin an ceto jam'iyyar daga rushewa.

"A halin yanzu muna fuskantar matsananciyar sauya sheka da ake yi zuwa jam'iyyarmu wanda ya hada da gwamnonin PDP," yace.

"Jam'iyyar yanzu ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali fiye da yadda muka tarar da ita. Duk da an fara samun tsoro, wayar da kai da aka dinga yi yasa tsoron ya fita daga zukatan mambobin jam'iyyar.

"Mun gano cewa matasa da mata sune suka fi yawa a bangaren zabe. Hakan yasa muka kafa kwamitin matasa da mata tare da masu nakasa."

A wani labari na daban, shugabar kwalejin koyar da jinya tare da ungwan zoma, Rukaiya Shettima Mustapha ta samu takardar tuhuma a kan dakatar da wasu dalibai da tayi kan cewa basu bi ayari sun fita tarar shugaba Buhari ba.

Legit.ng ta tattaro cewa Juliana Bitrus, wacce ita ce kwamishinan lafiya ta jihar ta aike da wasikar tuhumar inda take bukatar karin bayani kan lamarin cikin sa'o'i 48.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel