Wata Sabuwa: Sojoji sun afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi

Wata Sabuwa: Sojoji sun afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi

  • Rundunar 'yan sanda ta kame wasu sojoji da suka afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi
  • Lamarin ya faru ne a jihar Osun, an kame sojojin ana kuma ci gaba da bincike a kan lamarin
  • Dama Sheikh Gumi ya yi zargin cewa, akwai alamaun sojoji da jami'an tsaro na baki da masu aikata laifuka

Wasu sojoji uku sun mamaye wani ofishin ‘yan sanda a Osogbo, babban birnin jihar Osun, don kubutar da wasu mambobin kungiyar asiri daga magarkamar ‘yan sanda, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, CP Wale Olokode, a ranar Alhamis, ya ce an kama sojojin ne yayin da suke kokarin sakin wadanda ake zargin.

Olokode, ta bakin jami’ar hulda da jama’a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Osun, Misis Yemisi Opalola, ta ce an kame sojojin wanda tuni aka tsare su.

KU KARANTA: Bayan Mutuwar Kwamishinoni 2, An Fara Addu'o'in Neman Tsari a Jihar Ebonyi

Wata Sabuwa: Sojoji sun afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi
Jami'in dan sanda a bakin aiki | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

A cewarta:

“Sojojin uku sun mamaye ofishinmu da ke yankin Obelawo kusa da hanyar Ikirun a cikin Osogbo don kubutar da wasu ‘yan kungiyar asiri da 'yan sanda suka kama.

Ta kara da cewa sashen yaki da kungiyoyin asiri na ‘yan sanda ya dakile yunkurin, ya kame sojoji tare da tsare su a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID).

Ta kuma ce za a gudanar da bincike kan lamarin yadda ya kamata kuma za a dauki matakan da suka dace bayan binciken.

Yadda 'yan bindiga ke samun makamai daga jami'an tsaro, Sheikh Gumi ya yi zargi mai karfi

Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi zargin cewa akwai hadin baki tsakanin 'yan fashi da jami'an tsaro.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Gumi yayi wannan zargin ne a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, yayin wata hira da shi a gidan talabijin na Arise TV.

Gumi ya yi ikirarin cewa 'yan fashi suna samun makaman da jami'an tsaro ke rike da su Ya yi ikirarin cewa hukumomin tsaro na ba 'yan ta'adda damar mallakar tarin kayan makamai da suke rike da shi.

KU KARANTA: Ba Ni Ku Ke Cutarwa Ba: Lai Mohammed Ya Bayyana Illolin VPN Wajen Hawa Twitter

Sojoji sun karyata Sheikh Gumi kan cewa jami'ansu na hada baki da 'yan bindiga

A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta karyata zargin Sheikh Ahmad Gumi na cewa jami’anta suna hada baki da ‘yan bindiga wadanda suka kasance masu aikata laifuka daban-daban da cin zarafin da ake yi wa 'yan Najeriya.

Daraktan, Hulda da Jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya mai da martani ga zargin da Gumi ya yi a shirin ARISE TV Morning Show a ranar Laraba, Daily Trust ta tattaro.

Mista Nwachukwu ya ce sojojin Najeriya sun kasance wata alama ta hadin kan kasa mai sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata bisa mafi kwarewar aiki daidai da tsarin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel