A Cire Tallafin Man Fetur Sai Najeriya Ta Ci Gaba, Minista Ya Fadi Dalilai

A Cire Tallafin Man Fetur Sai Najeriya Ta Ci Gaba, Minista Ya Fadi Dalilai

  • Ministan Albarkatun man fetur ya bayyana bukatar kara farashin man fetur saboda kasa ta ci gaba
  • A cewarsa, Najeriya ba ta amfana da komai daga kokarin da take yi na jigila da kasuwancin man fetur
  • A cewarsa, kasar asara take tafka wa a kowane lokaci idan ta samar da man fetur ga 'yan Najeriya

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya sake nanata bukatar sake fasalta sashen man fetur ta hanyar sanya farashin kayayyaki kamar yadda kasuwa ke bi don bunkasa tattalin arzikin kasar.

Mista Sylva ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a taron Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba

A cire tallafin man fetur idan ana so Najeriya ta ci gaba, minista ya bayyana dalilai
Karamini minsitan man fetur na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake bayyana dalilansa na cewa dole a cire tallafin, ministan cewa ya yi:

“Zan iya cewa matsaya ta a kan tallafin mai da sake fasali sanannu ne. Na yi imanin cewa domin wannar kasa ta ci gaba, domin tattalin arzikinmu ya samu ci gaban da ake so, muna bukatar tsayar da farashin kayayyakin mai kamar yadda suke a kasuwa.
“Lokacin da kuka samar da wani abu a wani akan farashi mai tsada kuma kuka sayar da shi a farashi mai sauki ga mutane saboda kuna dauke wa mutane wasu nauyin da ke kansu ba shi ne mafi kyau ba.
“Abu ne da ake matukar so, amma kuma ba mai dorewa ba ne saboda abin da ke faruwa shi ne ku samar da abu a N10, ku sayar da shi N5; gobe, ku sake nemo shi a N10, ku kara N5 daga wani wuri, ku sake samar da shi a N10 ku siyar da shi kan N5.
"Don haka, asarar tana karuwa kuma tana hauhawa a kowace rana kuma wannan asarar da ake yi ita ta kawo mu inda muke."

Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

Gwamnatin tarayya ta ƙara jaddada wa yan Najeriya cewa su shiryawa ƙarin farashin man fetur saboda matsin tattalin arziƙin da ƙasar ke ciki.

Karamin ministan mai, Chief Timipre Sylva, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wajen yaye ɗalibai da basu kyaututtuka a jami'ar Patakwal, jihar Rivers.

Sylva yace nan bada jimawa ba gwamnati zata zare tallafin man fetur, wanda a cewarsa wasu yan kasuwa ne kaɗai ke amfanaa da tallafin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Kamar Yadda Gwajin HIV Yake Dole Kafin Aure, Haka Ma Na Shan Kwayoyi, Buba Marwa

A wani labarin, Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), ta ce noman shinkafa a kasar ya karu daga tan miliyan biyu a 2015 zuwa tan miliyan tara a 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce duba da yawan kayan da ake sarrafawa a yanzu, Najeriya ta shirya zama kasar da zata ke fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.

A cewarsa:

“Kafin zuwan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, mun saba samar da kimanin shinkafa tan miliyan biyu a shekara.
“A yau, za mu iya alfahari da tan miliyan tara a shekara; akwai bambanci sosai kuma yanzu za mu iya cewa balo-balo Najeriya ta wadatu da shinkafa.''

Asali: Legit.ng

Online view pixel