Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari

Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari

  • Tsohon dan sandan Amurka, Derek Chauvin ya samu hukuncin shekaru 22 da wata 6 a gidan yari
  • An yanke wannan hukuncin ne a ranar Juma'a bayan samun shi da laifin kisan George Floyd da aka yi
  • Chauvin ya kashe Floyd a ranar 25 ga watan Mayun 2020 bayan ya danne masa kai da guiwa kuma ya kai shi kasa

Derek Chauvin, tsohon dan sandan Amurka, ya samu hukuncin shekaru 22 da watanni shida a gidan yari sakamakon kashe bakar fata George Floyd da yayi.

A yayin yanke hukunci a ranar Juma'a, alkali Peter Cahill, ya ce an yanke wannan hukuncin ne ba don jin ta bakin jama'a ba, The Cable ta ruwaito.

"Hukuncin ba an yi shi bane domin tausasawa ba amma har ila yau ina son bada hakuri kan tsananin bakin ciki da kuna da iyalansu suke ciki, ballantana iyalan Floyd. Ina jinjina muku kuma ina jin kunar da kuke ji," Alkalin yace.

KU KARANTA: A daren farko, amarya mai shekaru 18 ta sheka lahira suna tsaka da soyewa da ango

Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari
Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Biloniyoyi 5 a Najeriya da jimillar dukiyarsu za ta iya fitar da kowa a kasar daga fatara

"Ban yanke hukunci saboda ra'ayin jama'a ba. Ban yi ba kuma domin wani yunkuri na tura sako ba, sai don dalilan da aka gabatar."

Floyd ya rasu a ranar 25 ga watan Mayun 2020 bayan Chauvin yayi ajalinsa ta hanyar kai shi kasa tare da saka guiwarsa a wuyansa lokacin da ya kama shi kan zarginsa da ake da kashe kudin jabu a wani shago.

Bidiyon da Floyd ke rokonsa inda yake cewa, "Bana iya numfashi," ya yadu a kafafen sada zumunta kuma ya janyo gagarumin zanga-zanga a ciki da wajen Amurka.

Bincikar gawar Floyd da aka yi an gano cewa mutuwarsa tana da alaka da wannan shakewar a wuyansa, CNN ta ruwaito.

A yayin shari'ar, iyalan Floyd sun ce suna son a tsananta hukunci wanda shine shekaru 40, amma masu gabatar da kara sun bukaci shekaru 30.

A yayin jawabi kafin yanke hukuncin, Chauvin ya mika gaisuwar ta'aziyyarsa ga iyalan Floyd.

"Ina son mika gaisuwar ta'azaiyyata ga iyalan Floyd. Akwai wasu labarai nan gaba da zaku so ji kuma ina fatan hakan zai kwantar muku da hankali. Nagode," tsohon dan sandan yace.

Hukuncin da aka yanke ranar Juma'a ya zo ne bayan alkalin kotun Minnesota ya kama Chauvin da laifuka uku na kisa da ake zarginsa dasu.

A wani labari na daban, shugabar kwalejin koyar da jinya tare da ungwan zoma, Rukaiya Shettima Mustapha ta samu takardar tuhuma a kan dakatar da wasu dalibai da tayi kan cewa basu bi ayari sun fita tarar shugaba Buhari ba.

Legit.ng ta tattaro cewa Juliana Bitrus, wacce ita ce kwamishinan lafiya ta jihar ta aike da wasikar tuhumar inda take bukatar karin bayani kan lamarin cikin sa'o'i 48.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel