Biloniyoyi 5 a Najeriya da jimillar dukiyarsu za ta iya fitar da kowa a kasar daga fatara

Biloniyoyi 5 a Najeriya da jimillar dukiyarsu za ta iya fitar da kowa a kasar daga fatara

Najeriya tana da tarin jama'a masu hannu da shuni da suka samu shuhura da nasibinsu ta hanyar kasuwanci. Ta yuwu hakan ce ta sa jama'a da dama suke ganin kasuwanci a mabudin arziki.

Wasu daga cikin biloniyoyin Najeriya sun shiga cikin jerin masu arziki na mujallar Forbes. A wannan rahoton, Legit.ng ta lalubo muku biloniyoyi biyar da kuma yawwan dukiyarsu.

KU KARANTA: Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu

Biloniyoyi 5 a Najeriya da jimillar dukiyarsu za ta iya fitar da kowa a kasar daga fatara
Biloniyoyi 5 a Najeriya da jimillar dukiyarsu za ta iya fitar da kowa a kasar daga fatara. Hoto daga @femiotedola, @aliko_dangotegcon, @tonyelumelu, @mikeadenugafamily
Asali: Instagram

KU KARANTA: Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram

A wani rahoto na Oxfam a 2016, an ce jimillar dukiyarsu za ta iya kawo karshen fatarar dake kasar nan baki daya.

1. Alike Dangote

Dan kasuwan shine na sahun gaba a arziki a Afrika a jerin sunayen da Forbes ta fitar. Yana da arzikin da ya kai N4,714,310,000,000 a yanzu haka kamar yadda Forbes ta sanar.

Dangote na hango mamaye kasuwar man fetur daga yadda ya gina sabuwar matatarsa.

2. Femi Otedola

Femi shine wanda yafi kowa hannun jari a Forte Oil, kamfanin da ke da daruruwan gidajen mai a fadin kasar nan.

A 2016, Forbes tace kudin Femi ya kai N737,892,000,000 kuma har a halin yanzu babu abinda ya canza daga dukiyarsa.

3. Folorunsho Alakija

Ita ce mataimakiyar shugaban Famfa Oil kuma tana da dukiyar da ta kai N409,940,000,000 a 2020 kamar yadda Forbes ta bayyana. Amma kuma a 2021, darajarta ta ragu saboda yadda farashin man fetur ya dinga faduwa.

Ta samu lasisinta ne a 1993 daga gwamnatin Najeriya kuma ta mallaki Agbami tun 2008.

4. Mike Adenuga

Gagarumin mai kudin kuma shahararre a fannin sadarwan yana da arzikin da ya kai N2,582,622,000,000 yanzu haka.

Ya taba aiki a matsayin direban tasi yayin da yake daukar nauyin kansa yana dalibi mai digiri na biyu a jami'ar Pace dake New York

5. Tony Elumelu

A 2017, kudinsa kamar yadda Forbes ta bayyana ya kai N286,958,000,000. Yana da manyan hannayen jari a fannin sadarwa kuma yana daga cikin shugabannin UBA.

A wani labari na daban, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci wata kungiyar siyasa da kungiyar shugabannin matasa ta arewa, da su bashi makonni uku domin tattaunawa tare da yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Laraba lokacin da aka gabatar masa da wasikar bukatarsa da ya tsaya takarar shugabancin kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Mambobin NYLF da suka samu jagorancin shugabansu na kasa Elliot Afiyo, sun gana da gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel