Gwamnatin Borno ta dauka mataki kan dakatar da dalibai saboda basu tari Buhari ba

Gwamnatin Borno ta dauka mataki kan dakatar da dalibai saboda basu tari Buhari ba

  • Gwamnatin jihar Borno tayi martani kan dakatar da daliban Najeriya da aka yi daga karatu saboda basu fita tarar Buhari a Borno ba
  • Juliana Bitrus, kwamishinan lafiya ta jihar ta bada takardar tuhuma a mika ga shugaban kwalejin koyar da jinya da ungwan zoma
  • Idan zamu tuna an baiwa wasu dalibai takardar dakatarwa daga karatu na mako daya saboda basu fita tarar Buhari ba a ziyarar da ya kai Borno

Jihar Borno

Shugabar kwalejin koyar da jinya tare da ungwan zoma, Rukaiya Shettima Mustapha ta samu takardar tuhuma a kan dakatar da wasu dalibai da tayi kan cewa basu bi ayari sun fita tarar shugaba Buhari ba.

Legit.ng ta tattaro cewa Juliana Bitrus, wacce ita ce kwamishinan lafiya ta jihar ta aike da wasikar tuhumar inda take bukatar karin bayani kan lamarin cikin sa'o'i 48.

KU KARANTA: Borno: Kwaleji ta dakatar da daliba saboda bata fita tarbar Buhari ba

Borno: Kwamishina na tuhumar shugaban makaranta da ta dakatar da dalibai kan Buhari
Borno: Kwamishina na tuhumar shugaban makaranta da ta dakatar da dalibai kan Buhari. Hoto daga Gov Borno
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke direba, sun sace mai ciki da mutum 32 a Kachia

Gwamnatin Borno ta nisanta kanta daga dakatar da daliban

Wannan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni.

A wasikar mai kwanan wata 25 ga Yuni, Juliana ta nisanta gwamnatin jihar daga matakin da Mustapha ta dauka inda tace ta yi aikin ne ta gaban kanta.

Kwamishinan ta kwatanta lamarin da ya faru da mara dadi, inda ta kara da cewa wannan hukuncin tayi shi ne babu tuntubar kowa balle ma'aikatar lafiya.

Ta ce shiga ayari a tari shugaban kasa abu ne da dalibai suka saba amma babu wanda ya taba matsa musu yin hakan.

Kwamishinan ta nuna jimaminta inda tace shugabar kwalejin tayi amfani da zuwan shugaban kasar ne inda ta kai ga wasu dalibai da take hari.

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ba za ta sassauta ba wurin kokarinta na ganin ta tabbatar da tsaro a kasar nan.

Osinbajo ya sanar da hakan ne a wata takarda da mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasan ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni kuma Legit.ng ta gani.

Ya ce kasafin da aka turawa majalisar tarayya an yi hakan ne domin karfafa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel