Da Ɗuminsa: PDP Ta Rushe Majalisar Shugabanninta Awanni Kaɗan Kafin Zaɓe
- PDP ta sallami dukkan shugabanninta reshen jihar Anambra tare da shugabannin ƙananan hukumomi
- Jam'iyyar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke a FCT Abuja
- Wannan na zuwa awanni ƙaɗan kafin zaɓen fidda ɗan takara da jam'iyyar PDP ta shirya ranar 26 ga watan Yuni
Jam'iyyar PDP ta rushe majalisar zartarwarta na reshen jihar Anambra gabanin zaɓen gwamna da za'a gudanar ranar 6 ga watan Nuwamba, kamar yadda premium times ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Tawagar Yan Ƙwallon Najeriya da Kyautar Sabbin Gidaje
Jam'iyyar ta umarci kwamitin riƙo na yankin Kudu-Gabas da ya kula da al'amuran jihar Anambra kafin a zaɓi sabbin shugabanni.
Wannan matakin yazo kwana ɗaya kacal kafin zaɓen fidda gwani a zaɓen gwamna da jam'iyyar ta shirya ranar 26 ga watan Yuni.
Kakakin PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Jumu'a.
Yace: "Mun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan hukuncin da babbar kotu ta yanke a akan shugabannin."
"Shirin da aka yi na fidda ɗan takarar gwamna a zaɓen dake tafe a jihar yana nan ba'a sauya komai ba."
Kotu ta sallami shugabannin jiha da na ƙananan hukumomi
A kwanan nan ne, wata babbar kotu dake zamanta a Abuja, ta yanke hukuncin sallamar shugabannin PDP reshen Anambra tare da na ƙananan hukumomi.
KARANTA ANAN: Ma'aikatan SPW: Mun Kammala Biyan Akalla Mutum 400,000 Haƙkinsu Na N60,000, Keyamo
Mamba a PDP, Samuel Anyakola, shine ya shigar da ƙara gaban kotu yana ƙalubalantar shugabannin jam'iyyar PDP na jihar da na ƙananan hukumomin tare da wakilan jiha da aka bayyana yayin gangamin PDP a yankin Kudu-Gabas.
Kotun ta kori dukkan shugabannin jihar, sannan ta umarci jam'iyyar ta yi amfani da wakilanta na 2017 wajen gudanar da zaɓen fidda ɗan takara.
A wani labarin kuma Mun Ɗauki Tsauraran Matakai Ta Yadda Ba Za'a Sake Kai Hari Makarantun Mu Ba, Gwamnatin Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro a makarantun jihar, kamar yadda daily trust ta ruwaito.
Kwamishinan jin ƙai da walwala, Hajiya Hafsat Baba, ita ce ta bayyana haka a wurin wani taron da ma'aikatarta ta shirya.
Asali: Legit.ng