Osinbajo ya bayyana sabon salon FG na kawo karshen 'yan bindiga da masu satar mutane

Osinbajo ya bayyana sabon salon FG na kawo karshen 'yan bindiga da masu satar mutane

  • Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya na matukar kokarin ganin bayan rashin tsaro
  • Osinbajo ya sanar da hakan ne a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa yayin da basaraken Ekiti ya kai masa ziyara
  • Kamar yadda yace, sarakunan gargaji, gwamnatocin kananan hukumomi da na jihar dole ne su hada kai da na tarayya

Aso Villa, Abuja

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ba za ta sassauta ba wurin kokarinta na ganin ta tabbatar da tsaro a kasar nan.

Osinbajo ya sanar da hakan ne a wata takarda da mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasan ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni kuma Legit.ng ta gani.

Ya ce kasafin da aka turawa majalisar tarayya an yi hakan ne domin karfafa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro a kasar nan.

KU KARANTA: Shugabancin kasa a 2023: Gwamnan Bauchi yace yana tuntubar masu ruwa da tsaki

Osinbajo ya bayyana sabon salon FG na kawo karshen 'yan bindiga da masu satar mutane
Osinbajo ya bayyana sabon salon FG na kawo karshen 'yan bindiga da masu satar mutane. Hoto daga Laolu Akande
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram

Mataimakin shugaban kasan yace wannan kasafin kudin yana daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na shawo kan kalubalen tsaro da ya addabi kasar nan.

Ya sanar da hakan a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni lokacin da Oluyin na Iyin Ekiti, Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye ya kai masa ziyara har fadar shugaban kasa dake Abuja.

Akande ya ce ministan masana'antu, cinikayya da hannayen jari, Otunba Niyi Adebayo da Sanata Opeyemi Bamidele suun halarci ganawar.

Gwamnatin tarayya na bukatar hadin kai daga sarakuna

Osinbajo ya kara da jaddada cewa dole ne sarakunan gargajiya, gwamnatocin kananan hukumomi da na jiha su hada kai da gwamnatin tarayya wurin shawo kan matsalar tsaro.

Ya ce: "A cikin kwanakin nan ne aka kafa kwamitin duba yanayin tsaro domin duba bukatar rundunar soji tare da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

"Hakan ce ta sa aka mika wani kasafi gaban majalisar tarayya. Dalilin haka kuwa shine mika bukatar sojojin tare da sauran hukumomin tsaro domin su dage wurin shawo kan matsalar tsaro a kasar nan."

A wani labari na daban, a kalla mutum daya aka kashe kuma aka sace 33 bayan harin da wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Channels Tv ta ruwaito, lamarin ya faru ne a daren jiya a cikin garin Kachia kuma hakan ya bar jama'a da dama da raunika.

Hakimin Kachia, Idris Suleiman ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da jami'an tsaro da suka samu jagorancin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel