Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke direba, sun sace mai ciki da mutum 32 a Kachia

Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke direba, sun sace mai ciki da mutum 32 a Kachia

  • Miyagun 'yan bindiga sun halaka direba tare da sace wasu mutum 33 a garin Kachia dake jihar Kaduna
  • Kamar yadda hakimin garin mai suna Idris Suleiman ya bayyana, miyagun sun hada da wata mai juna biyu sun tafi
  • Sun shiga garin ne a cikin daren Laraba inda suka dinga harbi tare da kwashe kayan shaguna yayin da 'yan kasuwa ke gudu

A kalla mutum daya aka kashe kuma aka sace 33 bayan harin da wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Channels Tv ta ruwaito, lamarin ya faru ne a daren jiya a cikin garin Kachia kuma hakan ya bar jama'a da dama da raunika.

Hakimin Kachia, Idris Suleiman ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da jami'an tsaro da suka samu jagorancin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

KU KARANTA: Garba Shehu ya ce Buhari ne tauraron damokaradiyyar Najeriya

Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke direba, sun sace fasinjoji 33 a Kachia
Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke direba, sun sace fasinjoji 33 a Kachia. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu

Suleiman ya ce 'yan bindigan masu tarin yawa sun kutsa yankin wurin karfe 9 na daren Laraba kuma sun fara harbi babu kakkautawa a kokarinsu na tsorata mazauna yankin.

Yayi bayanin cewa 'yan bindigan sun kai hari wani gidan biredi inda suka sace mutum biyar tare da kashe direban mai gidan biredin kafin su karasa wani yanki da ake kira da Mother Cat inda suka sace mutum 28 tare da wata mai juna biyu.

Kamar yadda yace, 'yan bindigan sun debe kayan shaguna dake cikin garin bayan 'yan kasuwa sun tsere sun bar shagunansu, Chronicles ta ruwaito.

A cikin kwankin nan 'yan bindiga sun gallabi jihar Kaduna inda suke kashe jama'a tare da yin garkuwa da wasu har da daliban makarantu.

Wannan harin Kachia yana zuwa ne bayan kwanaki kadan da wasu miyagun 'yan bindiga suka harbe dagacin kauyen Dogon Daji dake karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna mai suna Mallam Anja.

Makasan sun kai samame kauyen ne inda suka shiga har gidan dagacin suka dinga harbinsa har ya mutu.

A wani labari na daban, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci wata kungiyar siyasa da kungiyar shugabannin matasa ta arewa, da su bashi makonni uku domin tattaunawa tare da yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Laraba lokacin da aka gabatar masa da wasikar bukatarsa da ya tsaya takarar shugabancin kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Mambobin NYLF da suka samu jagorancin shugabansu na kasa Elliot Afiyo, sun gana da gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel