Borno: Kwaleji ta dakatar da daliba saboda bata fita tarbar Buhari ba

Borno: Kwaleji ta dakatar da daliba saboda bata fita tarbar Buhari ba

  • Wata dalibar Najeriya ta samu takardar dakatarwa daga kwaleji bayan an gano cewa bata je tarbar shugaba Buhari ba kamar sauran dalibai
  • An mika wa dalibar takardar shaidar dakatarwa ta mako daya kuma an sanar da ita ta dawo mako na gaba tare da iyayenta
  • Wannan lamarin ya janyo maganganu daban-daban a kafafen sada zumunta inda aka dinga zagin makarantar a kan hakan

An baiwa wata dalibar Najeriya takardar dakatarwa daga kwaleji saboda bata fito tarar shugaban kasan Najeriya ba a ziyarar da ya kai jihar Borno a ranar 17 ga watan Yuni.

Wani shafi mai amfani da Instabog9ja ya wallafa takardar dakatarwan wacce ta fara aiki daga ranar 21 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun tasa keyar tsohon dan majalisa Farouk zuwa gidan yarin Kuje

Borno: Kwaleji ta dakatar da daliba saboda bata fita tarbar Buhari ba
Borno: Kwaleji ta dakatar da daliba saboda bata fita tarbar Buhari ba. Hoto daga @instablog9ja, afriuni
Asali: Instagram

KU KARANTA: Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu

Dakatarwan za ta kai har na mako daya. A wata takardar da kwalejin koyar da jinya da ungwan zoma ta Maiduguri ta fitar, an umarci dalibar da ta dawo mako na gaba da iyayenta.

Har a yayin rubuta wannan rahoton, ba a gano sunan dalibar da lamarin ya shafa ba.

Kafar sada zumunta ta caccaki makarantar

Ma'abota amfani da kafar sada zumunta sun harzuka da wannan matakin da makarantar ta dauka.

Mutane da yawa sun dinga mamakin yadda aka wajabta tarar shugaban kasa a makarantar kamar karatu.

@empress_efe ya rubuta: "Tarar shugaba Buhari ya zama karatu kenan??"

@kosh_toms tsokaci yayi da: "Shugaban kasan mene, nafi son a dakatar dani a kan tarar shi."

@sosamangram cewa yayi: "Wannan umarnin zababbu ne? Buharin nan mulkin mallaka yake."

@peterr_deee cewa yayi: "Ina dalibar take?? Za mu dauka nauyin karatunta zuwa kowacce jami'a da take so a kasar waje."

@adeoluolatomide martani tayi da: "Gara in yi maraba da akuyar kakata."

A wani labari na daban, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci wata kungiyar siyasa da kungiyar shugabannin matasa ta arewa, da su bashi makonni uku domin tattaunawa tare da yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Laraba lokacin da aka gabatar masa da wasikar bukatarsa da ya tsaya takarar shugabancin kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Mambobin NYLF da suka samu jagorancin shugabansu na kasa Elliot Afiyo, sun gana da gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng