An gano wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba

An gano wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba

  • An gano wani mutum mai mata da yawa a wani gari da ake kira Tenzuku a yankin Gabashin kasar Ghana inda yake da ‘ya’ya sama da 200
  • Da yake magana a wani karamin taron yaran da ke wurin, mai magana da yawun mutumin ya nuna cewa mutumin na da mata 43
  • An ruwaito cewa adadin yaran da aka bayyana sun yi kasa da ainihin adadin saboda ba a kidaya yara mata ba

An gano wani mutum wanda aka bayyana sunansa da Nana yana da yara sama da 200 tare da matansa 43 a yankin Gabashin Ghana.

Shirin safe na Angel TV (Anopa Bofo) ƙarƙashin jagorancin Kofi Adomah sun yi tattaki zuwa Tenzuku, ƙauyen da ake tukin awowi 13 daga Accra don yin hira da wasu daga cikin yaran babban gidan.

KU KARANTA KUMA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Kodayake mutumin da kansa bai halarci taron ba, amma mai magana da yawunsa ya nuna cewa kimanin matan da yaran da aka kiyasta ba su kai ainihin adadin ba.

Kalli cikakken bidiyon a kasa

A cewarsa, ba a kirga yawancin ‘ya’yansa mata saboda da zarar sun yi aure, sai su koma zama tare da mazajensu.

KU KARANTA KUMA: Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

'Yan asalin Tenzuku suna koina

Ya kuma bayyana cewa da wuya a sami wani wuri a Ghana da babu ɗan asalin Tenzuku, saboda da yawa sun yi kaura zuwa sassa daban-daban na ƙasar.

Akwai zaman lafiya

Mutumin ya kuma tabbatar da cewa dukka ahlin suna zaune lafiya, suna cin abinci daga junansu sannan kuma suna kula da ya’yan juna, duk da yawansu.

An gano wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba
Mutumin na da yara sama da 200 da matan aure 43 Hoto: YouTube, Angel TV Gh
Asali: UGC

Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40

A wani labarin, Nura Walwala Magaji kafinta ne mai shekaru 36 daga gundumar Zango ta karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi.

Ya ce yana alfahari da yadda ya haifa yara 13, maza 10 sai mata 3. Yana fatan cika burinsa na yarinta inda yake son haifar 'ya'ya a kalla 40.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, Magaji yana da mata hudu kuma kowacce ta haihu a cikin makonni uku. Ya ce kula da su ba zai zama matsala ba domin Allah ne ke kula da yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel