Marigayi kwamishinan Ebonyi ya farka daga mutuwar da yayi? Gwamna Umahi ya magantu
- Gwamna Dave Umahi ya mayar da martani game da rahotannin da ke cewa marigayi Fidelis Nweze kwamishinan more rayuwa ya dawo rayuwa
- A cikin wani gajeren bayani a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni, gwamnan Ebonyi ya bayyana karara cewa ikirarin na karya ne
- Umahi ya gargadi ‘yan kasa a jihar da su guji yayata labaran karya da rahotanni marasa tushe da za su haifar da radadi ga dangin mamacin
Akwai rahotannin da ba a tabbatar ba daga wasu kafofin yada labarai kamar Vanguard cewa Fidelis Nweze, marigayi kwamishinan kayayyakin more rayuwa a Ebonyi, wanda aka bayyana mutuwarsa kwanan nan, ya farfado.
Sai dai, gwamnatin jihar ta ba da rahoto a hukumance a matsayin martani ga labarin wanda tuni ya yadu har a wajen Ebonyi, jaridar The Cable ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: An gano wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni, Gwamna Dave Umahi ya karyata ikirarin a matsayin kanzon kurege kuma mara tushe.
Gwamnan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce babu wata hujja da zata nuna cewa marigayi Nweze ya tashi daga mutuwar da yayi, ya kara da cewa mutane su daina yada labaran karya wanda yake da alaka da irin wannan lamari mai matukar muhimmanci.
KU KARANTA KUMA: Shin Atiku dan Najeriya ne: Kotu ta sanya ranar sauraron karar da aka shigar
Umahi ya bayyana:
“Babu wata shaidar hoto ko tabbaci daga asibitin kuma muna tambaya me ya sa mutane za su shiga maganar ance-ance a wannan mawuyacin lokaci.
“Dole ne mu yarda da gaskiyar da ke gabanmu duk da cewa mutuwar mamacin tana da wuyar hadiyewa. Ya kamata mutane su daina yada labaran da ba a tantance su ba domin hakan na kara cutar da wadanda ke juyayi a halin yanzu.”
Bayan Mutuwar Kwamishinoni 2, An Fara Addu'o'in Neman Tsari a Jihar Ebonyi
A wani labarin, mun ji a baya cewa gwamnatin Ebonyi ta fara addu’ar neman kariya na kwanaki uku sakamakon mutuwar kwamishinoni biyu a jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Francis Nwaze, mai taimakawa na musamman ga Gwamna David Umahi kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Alhamis.
Addu’ar da aka yiwa lakabi da “Allah ya kare jihar mu da shugabannin mu’’ an shirya ta ne tare da kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar ta Ebonyi.
Asali: Legit.ng