An sanar da ranar da gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai koma APC

An sanar da ranar da gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai koma APC

  • Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Bello Matawalle zai koma jam'iyyar APC a ranar Talata 29 ga watan Mayu
  • Jami'ai a matakin kasa da jiha a jam'iyyar All Progressives Congress, APC sun ce sun shirya tsaf domin tarbar Matawalle a Gusau
  • Sai dai jam'iyyar PDP ta bakin kakakinta na kasa, Kola Ologbondiyan ta ce Matawalle bai sanar da ita ba cewa zai fice

Bayan kwashe watanni ana hasashe, ana sa ran Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, zai fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya koma All Progressives Congress, APC, a ranar Talata 29 ga watan Yuni, rahoton Daily Sun.

Sauya shekar nasa na zuwa ne kimanin wata guda bayan gwamnan Cross Rivers Ben Ayade ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ne na farko da ya fara barin PDP ya koma APC a farkon shekarar nan.

Sau da dama, hadiman Matawalle sun sha musunta zargin cewa zai sauya sheƙa.

A watan Afrilun da ta gabata, gwamnonin PDP sun gana da Matawalle sun roƙe shi kada ya bar jam'iyyar.

Daily Sun ta ruwaito cewa jami'ai a matakin ƙasa, jihohi da sauran jiha-jigan jam'iyyar APC sun shirya tsaf don tarbar gwamnan a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Martanin jam'iyyar PDP game da batun sauya shekan Matawalle

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa Kola Ologbondiyan, ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa ba a sanar da hedkwatar jam'iyyar batun sauya sheƙan ba a hukumance.

KU KARANTA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

"Bai rubuta mana wasika ba. A yadda aka saba, idan kai ɗan jam'iyyar mu ne kuma kana son fita, kamata ya yi ka sanar da mu a rubuce.

Gwamnan jihar Zamfara bai sanar da mu a rubuce cewa zai fita daga jam'iyyar mu ba.

"Don haka, ba za mu iya cewa mun san da batun fitarsa daga jam'iyyar ba," in ji Ologbondiyan.

Da aka tuntube shi, mashawarcin gwamnan na musamman kan kafafen watsa labarai, Zailani Bappa ya ce a dandalin sada zumunta kawai ya ji jita-jitar cewa mai gidansa zai sauya sheƙa.

"A hukumance, ba a sanar da ni ba don haka ba zan iya tabbatar wa ko ƙarya bane ko gaskiya ne," in ji shi.

A wani rahoton, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross Rivers ta bada kwangilar a siyo mata tsintsiya guda miliyan uku daga masu siyarwa a kasuwanni don sabbin mutanen da suka shiga jam'iyyar, Premium Times ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Bassey Ita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Calabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel