Shin Atiku dan Najeriya ne: Kotu ta sanya ranar sauraron karar da aka shigar
- Masu karar na neman Kotun da ta fayyace ko Atiku Abubakar yana da damar tsayawa takarar shugabancin kasa
- Suna da’awar ba a haife shi a cikin Najeriya ba
- Sai ranar 27 ga Satumba za a ci gaba da sauraron karar
Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja a ranar Alhamis ta sanya ranar 27 ga watan Satumba domin sauraron karar da wata kungiyar ta shigar gabanta inda take kalubalantar matsayin kasancewar tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar cikakken dan kasa.
Kungiyar ta shigar da karar tun 2019 inda take kalubalantar cancantar tsayawa takarar shugabancin kasa na Alhaji Atiku Abubakar.
A lokacin da aka karanto karar, lauyan masu shigar da karar Akinola Oladimeji ya fada wa kotun cewa bai shirya wa tunkarar karar ba tukuna.
Lauyan ya fada wa kotun cewa sai a ranar Laraba ne aka sanar da shi cewa za a saurari karar a ranar Alhamis tun bayan da a farko aka sanar masa cewa an dage zaman zuwa ranar 20 ga watan Satumba.
Alkalin, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya nemi sanin cewa ko an sanar wa dukkanin bangarorin biyu kan zaman da za a yi a yau daga bakin rajistara na kotun inda ya ce eh an sanar.
Daga nan sai alkalin ya nuna bacin ransa kan yadda ya ce ya saka ranar zaman wanda daga karshe ya zama abin ce-ce-ku-ce.
Sai dai daga bisani ya dage zaman zuwa ranar 27 ga watan Satumba tare da jan kunnen masu karar cewa wannan ne karo na karshe da za a dage sauraron karar.
KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun
DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN) ya ruwaito cewa masu karar wata kungiyar farar hula ce mai lambar rajista FHC/ABJ/CS/177/2019 ita ce ke kalubalantar zama dan kasa kan Atiku Abubakar bisa hujjar cewa ba a haife shi a Najeriya ba.
Hujjojinsu na ce ba dan Najeriya bane
Masu karar suna kalubalantar ne bisa wadannan ababuwan da suke da’awa a kansu cewa kotun ta yi hukunci a kai:
“Ko cewa Sashe na 25 na Kundin Tsarin Mulki shi ne kadai zai zama abin dogaro a hukumance wajen bayanin hanyoyin da mutum zai zama dan kasa shi ne kawai ta hanyar haifar mutum a kasa.
“Ko tanadin Kundin Mulki Sashe na 131(a) na Kundin Mulki, ya ce dan Najeriyar da aka haifa a kasar zai iya takarar shugabancin kasa.
“Ko fassarar Sassa na 25(1) (2) da 131(a) na Kundin mulkin, na nufin Jam’iyyar PDP da INEC za sun iya tantance shi Atikun wajen tsayawa takarar kujerar shugabancin kasa lura da inda aka haife shi.
Asali: Legit.ng