Katuwar Giwa ta Fada Gidan Wata Mata Neman Abinci, Jama'a Sun Dinga Mamaki
- Wata mata ta sha mamaki bayan ta tashi ta ga Giwa ta ballo ta shigo mata har cikin gida
- Giwa ta asalin yankin Asia ta bibiyi kamshin abinci ne dake madafi gidan matar inda ta kutsa kai ta wani rami
- Lamarin da ya faru a tsakar dare ya janyo maganganu a kafar sada zumunta yayin da jama'a da yawa suka nuna mamakinsu
Wata giwa ta kutsa cikin gidan wata mata neman abinci. Lamarin ya faru a tsakar daren ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2021.
Kamar yadda matar da lamarin ya shafa tace, giwar ta shiga gidanta ne ta wani rami dake madafinta wanda ba a gyara ba, CNN ta ruwaito.
KU KARANTA: Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara
KU KARANTA: Jami'an tsaro sun tasa keyar tsohon dan majalisa Farouk zuwa gidan yarin Kuje
An gano cewa giwar ta saka hancinta ne inda ta dinga dube-dube a madafin. Mazauniyar kasar Thailand din mai suna Ratchadawan Puengprasoppon ta ce: "Muna bacci yayin da muka ji sauti a madafi.
"Jin haka yasa muka gaggauta zuwa inda muka tarar da giwar ta saka hancinta a madafi inda ta fasa bango. Na saba ganin giwaye suna yawo a gari neman abinci tun ina karam. Amma wannan ne karon farko da suka lalata min gidana."
Kafar sada zumunta sun yi martani
CGTN ce ta wallafa hotunan lokacin da giwar ta shiga gidan kuma ta janyo cece-kuce.
Le Ozinuel cewa yayi: "Giwar kamata yayi ta zauna a gidan namun daji. Duk da muna da rakumin dawa da giwaye da yawa dake yawo a Afrika, amma muna adana su a inda ya dace."
Agbelekale Medinat Abimbola tsokaci yayi da cewa: "Nagode Ubangiji da ba giwar dake gaban First Bank bace. Me zai faru da 5200 dita idan giwar ta hadiya."
A wani labari na daban, babban mataimakin shugaban kasa Buhari a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da tauraron damokaradiyya a Najeriya.
Shehu ya yi wannan tsokacin a ranar Talata, 22 ga watan Yuni yayin jawabi a wani kaddamar da littafi wanda wakilin Legit.ng ya halarta a Abuja.
Mai magana da yawun shugaban kasa ya kwatanta littafin da cewa shugaban kasa Buhari aka kwatanta a dunkule, inda ya kara da cewa mawallafin, Abdullahi Haruna yayi aiki tukuru inda ya saukakawa masu magana da yawun shugaban kasan ayyukansu da abinda littafin ya kunsa.
Asali: Legit.ng