Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum

Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum

  • Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa na maida yan gudun hijira zuwa gidajen su ne saboda su yi noma
  • Gwamnan yace an samu nasara sosai a ƙoƙarin da ake na inganta rayuwar yan gudun hijira a jiharsa
  • Yace sam baya tsoron mutuwa domin rai guda ɗaya gare shi, kuma idan lokacinsa yayi zai tafi

Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, yace gwamnatinsa na maida yan gudun hijira gidajensu ne domin su noma gonakinsu, su taimaka wajen daƙila ƙarancin abinci, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ganduje: Aikin Ta'addanci a Najeriya Ya Shiga Mataki Na Gaba 'Next Level'

Mr. Zulum yayi wannan jawabi ne a wata fira da ya yi da BBC Hausa ranar Alhamis.

Gwamnan yace yan gudun hijira aƙalla 10,000 daga Damasak, waɗanda suka bar ƙauyukan noman su a jihar Borno, yanzun sun koma gidajen su.

Farfesa Babagana Umaru Zulum, Gwamnan Jihar Borno
Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamna Zulum ya ƙara da cewa akwai buƙatar mutanen su koma asalin garuruwansu domin su yi noma.

"Mun maida yan gudun hijira zuwa garuruwansu da suka haɗa da Dikwa, Baga, da sauransu waɗanda rikicin Boko Haram ya raba da mahallansu," inji Zulum.

Yace mutane sun koma gidajen su ne domin su cigaba da noma da sauran kasuwancin su kamar yadda suka saba a baya.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook

Ba na tsoron mutuwa, shiyasa nake ziyartar ko ina a cikin Mota, Zulum

Gwamna Zulum yace ya gujewa hawa jirgi yayin ziyartar yankunan dake cikin tashin hankali, saboda ya gane wa idanunsa yadda lafiyar hanyoyi take.

"Meyasa zamu ji tsoron yin tafiya a hanyar mota? Rai guda ɗaya muke da shi kuma Allah ne yake yanke lokacin mutuwar mutum. Wannan ke ƙara mun ƙwarin guiwar zuwa yankin da ake tashin hankali a cikin mota." Zulum ya faɗa.

A wani labarin kuma Sanatoci Zasu Bayyana Sunayen Ma'aikatu, Hukumomin da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

A ranar Talata, Sanatoci sun sha alwashin zasu fara bayyana sunayen ma'aijatu, sashi-sashi da hukumomi (MDAs) na gwamnatin tarayya waɗanda suka kasa kare tuhumar da ofishin Adita Janar na ƙasa (AuGF) ya musu.

Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, shine ya nuna haka bayan an gabatar da rahoton kwamitin kula da asusun fili.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel