Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB Ta Fara Sakin Sakamakon Jarabawar UTME 2021

Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB Ta Fara Sakin Sakamakon Jarabawar UTME 2021

  • Hukumar JAMB ta saki sakamakon jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta bana UTME 2021
  • Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyade, shine ya bayyana haka a taron manema labarai a jihar Ebonyi
  • Oloyade yace a halin yanzun an kusa kammala jarabawar baki ɗaya, kuma babu dalilin da zaisa su rike wa ɗalibai sakamakon su

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB, tace zata fara sakin sakamakon jarabawar UTME 2021 daga ranar Laraba 23 ga watan Yuni, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Mun Gano Wani Mummunan Shiri da Aka Shirya Mana Kan Jarabawar Bana 2021, Shugaban JAMB

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyade, shine ya bayyana a wurin taron manema labarai a jihar Enugu.

Oloyade yace hukumar ba ta da wani dalili da zai sanya ta riƙe sakamakon jarabawar da ɗalibai suka kammala.

JAMB Ta Fara Sakin Sakamakon Jarabawar UTME 2021
Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB Ta Fara Sakin Sakamakon Jarabawar UTME 2021 Hoto: jamb.gov.ng
Asali: UGC

Yace: "Ya kamata ace yanzu an saki sakamakon waɗanda suka yi tasu jarabawar, amma saboda bana Hedkwata hakan bai samu ba, kuma bana son in amince a fitar da sakamakon yayin da nake waje."

"Amma da zaran na koma Abuja yau, dukkan jarabawar da aka yi harda ta yau, zamu sake ta, domin bamu da dalilin riƙe ta."

KARANATA ANAN: Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum

Mun zo nan ne domin duba yadda jarabawar ke gudana, shugaban JAMB

Shugaban JAMB, Farfesa Oloyade, yace tawagarsa taje yankin kudu maso gabas ne domin duba yanayin yadda jarabawar bana ke gudana, sannan kuma sukai ziyara sabuwar jami'ar Ebonyi.

Oloyade ya bayyana cewa ɗalibai 1,415,501 ne suka yi rijistar zana jarabawar UTME 2021, kuma a halin yanzun mutum 1,122,095 sun kammala, sauran 66,111.

A wani labarin kuma Sanatoci Zasu Fallasa Sunayen MDAs da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

Sanatoci zasu fara bayyana duk wata hukuma ko ma'aikatar gwamnati da ta gaza kare zargin da ake mata, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban Sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, shine ya bayyana haka bayan gabatar da rahoton kwamiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel