Cikakken Bayani: Sanatoci Zasu Fallasa Sunayen MDAs da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

Cikakken Bayani: Sanatoci Zasu Fallasa Sunayen MDAs da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

  • Sanatoci zasu fara bayyana duk wata hukuma ko ma'aikatar gwamnati da ta gaza kare zargin da ake mata
  • Shugaban Sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, shine ya bayyana haka bayan gabatar da rahoton kwamiti
  • Kwamitin ya bayyana cewa wasu daga cikin ma'aikatu sun kasa kare tuhumar da ofishin AuGF ya musu

A ranar Talata, Sanatoci sun sha alwashin zasu fara bayyana sunayen ma'aijatu, sashi-sashi da hukumomi (MDAs) na gwamnatin tarayya waɗanda suka kasa kare tuhumar da ofishin Adita Janar na ƙasa (AuGF) ya musu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Dagaci da Matarsa a Ibadan

Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, shine ya nuna haka bayan an gabatar da rahoton kwamitin kula da asusun fili.

Majalisar dattijan Najeriya
Da Ɗuminsa: Sanatoci Zasu Bayyana Sunayen Ma'aikatu, Hukumomin da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamitin ya gabatar da rahotonsa ne a kan binciken da ya gudanar bayan ofishin AuGF ya fitar da rahoto a shekarar 2015.

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide, a yayin gabatar da rahoton yace wasu daga cikin MDAs sun gaza kare kansu akan zargin da ofishin AuGF ya musu.

KARANTA ANAN: Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace

Sanata Urhoghide, Yace: "Da yawan ma'aikatun gwamnatin tarayya da hukumoni sun ƙi zuwa su kare kansu kan tuhumar ɓatar wasu kuɗaɗe da ofishin AuGF ya fitar a rahotonsa."

A wani labarin kuma Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook

Wani fitaccen malamin addinin musulunci yace haramun ne amfani da alamar dariya a facebook domin muzgunawa wani, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

Malamin mai amfani da suna ɗaya, Ahmadullah, yana da tarin mabiya a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel