Mun Gano Wani Mummunan Shiri da Aka Shirya Mana Kan Jarabawar Bana 2021, Shugaban JAMB

Mun Gano Wani Mummunan Shiri da Aka Shirya Mana Kan Jarabawar Bana 2021, Shugaban JAMB

  • Shugaban hukumar JAMB, Farefesa Ishaq Oloyade, yace bara gurbin mutane sun ƙulla shirin kaiwa hukumar hari
  • Yace an haɗa baki da wasu ma'aikatan wucin gadi na JAMB domin yi wa JAMB fashin amsoshin jarabawa
  • Duk wani mai hannu a wannan maƙarkashiya zamu kamo shi, kuma zai fuskanci hukunci a cewar Oloyade

Ƙalubalen satar jarabawa a Najeriya yana ƙara ɗaukar sabon salo yayin da shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa an shirya kai harin fashi don a sace tambayoyin jarabawa.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook

Shugaban JAMB yace wasu mutane sun haɗa baki da ma'aikatan wucin gadi, inda suka shirya yadda zasu kai hari kan hukumar JAMB domin satar jarabawa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Satar jarabawar JAMB
Mun Gano Wani Mummunan Shiri da Aka Shirya Mana Kan Jarabawar Bana 2021, Shugaban JAMB Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Prof. Oloyede ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin ƙasa da ƙasa dake Akanu-Ibiam, ranar laraba bayan kammala zagayen duba yadda jarabawar ke gudana a yankin kudu-gabas.

Yace: "Duk da matakan da JAMB ta ɗauka amma wasu mutane suna ganin suna da wayo, saboda haka zasu iya canza tsarin."

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Sanatoci Zasu Fallasa Sunayen MDAs da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

JAMB zata damƙe duk masu hannu a shirin kai mata hari

Shugaban JAMB ya kara da cewa hukumar ta fara shirye-shiryen yadda zata kamo duk masu hannu a kan wannan shirin na kai mata hari.

Yace: "Yanayin yadda ake kokarin satar amsoshin jarabawa a arewacin Najeriya, ya sha ban-ban da na kudanci."

"Abun da zamu ce a halin yanzu shine, duk wani dake barazanar hana mu sauke haƙƙinmu, zai fuskanci doka."

A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum

Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa na maida yan gudun hijira zuwa gidajen su ne saboda su yi noma, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Gwamnan yace an samu nasara sosai a ƙoƙarin da ake na inganta rayuwar yan gudun hijira a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: