Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe

Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe

  • Bayan ritayar tsoffin hafsohin tsaro a Najeriya, an nada su a matsayin jakadun Najeriya
  • An tura Janar Tukur Yusuf Burutai zuwa jamhuriyar Benin, yayin da sauran ma aka tura su wasu kasashe
  • Gwamnatin tarayya ta yi amfani da shafin ta Koo domin sanar da inda aka tura jakadun na Najeriya

Gwamnatin tarayya ta sanar da tura tsoffin shugabannin rundunonin soji a matsayin jakadun Najeriya a kasashen makwabta, jaridar Cable ta ruwaito.

Gwamnatin tarayya ta sanar da tura tsoffin shugabannin rundunonin ne ta hanyar amfani da asusun sada zumunta na Koo, wani dandamali na kasar Indiya, ranar Laraba.

Saddique Abubakar, tsohon hafsan hafsoshin sojin sama, an tura shi zuwa kasar Chadi haka kuma an tura Ibok-Ete Ibas, tsohon babban hafsan sojojin ruwa zuwa kasar Ghana.

KU KARANTA: Kamar almara: Beraye sun fatattaki wasu fursunoni da ma'aikata daga gidan yari

Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe
Yayin da aka tura tsoffin shugabannin rundunonin tsaro zuwa wasu kasashe a matsayin jakadu| Hoto: Government of Nigeria/Koo
Asali: UGC

Tun farko an tura Tukur Buratai, tsohon babban hafsan hafsoshin soja, zuwa Jamhuriyar Benin yayin da aka tura Abayomi Olonisakin, tsohon shugaban hafsoshin tsaro zuwa Jamhuriyar Kamaru.

An tura Sani Usman, tsohon hafsan tsaro zuwa Jamhuriyar Nijar.

Dalilin da yasa Shugaba Buhari ya nada tsoffin shugabannin rundunoni a matsayin jakadu

A watan Fabrairu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsoffin shugabannin rundunonin tsaro a matsayin jakadu bayan sun yi ritaya.

Duk da cewa wasu 'yan Najeriya sun soki nade-naden da aka yi wa tsofaffin shugabannin saboda lamuran da suka shafi tsaro a kasar amma fadar shugaban kasar ta tabbatar da nadin nasu, tana mai cewa tukuici ne ga aiki tukuru da suka yi.

Hakazalika, majalisa ba ta yi wata-wata ba wajen tabbatar da nadin nasu, lamarin da ya kara jawo cece-kuce, Vanguard ta ruwaito.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa:

"Shugaban yana ba da tukuici ne saboda aiki tukuru da sadaukarwa ta musamman daga wasu shugabannin sojoji wadanda suka ba da duk abin da suka ga kasa na bukata da za a tuna da shi."

KU KARANTA: Matawalle ya gana da Buhari, ya fadi yadda arewa ke farfadowa daga rashin tsaro

Da dumi-dumi: Bayan ritaya, an tura burutai wata kasa a matsayin ambasada

A wani labarin, Tsohon hafsan hafsoshin soja, Lt.Gen. Tukur Yusufu Buratai (rtd), an tura shi Jamhuriyar Benin a matsayin jakada, Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da Janar Abayomi Gabriel Olonisakin (rtd), tsohon Babban hafsan hafsoshin tsaro, aka nada a matsayin shugaban mishan zuwa kasar Kamaru.

A wani takaitaccen bikin da aka yi a Abuja ranar Talata, Ministan Harkokin Wajen, Geoffrey Onyeama, ya gabatar da wasikun amincewa da nadin tsofaffin shugabannin na tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel