Kamar almara: Beraye sun fatattaki wasu fursunoni da ma'aikata daga gidan yari

Kamar almara: Beraye sun fatattaki wasu fursunoni da ma'aikata daga gidan yari

  • Wasu beraye sun addabi wani gidan yarin kasar Australia lamarin da ya kai ga kwashe fursunoni
  • Berayen sun addabi gidan yarin ne tare da barnata wurare da dama na gidan cikin kankanin lokaci
  • Hukumar gidan yarin ya bayyana cewa, zai gudanar da gyara kafin daga bisani a dawo da fursunonin

A wani rahoto da jaridar The Guardian ta ruwaito, wasu beraye sun tilasta kwashe fursunoni daga wani gidan yari a kasar Australia bayan sun addabe su.

Sama da fursunoni 400 da ma'aikata 200 na gidan yarin Wellington a New South Wales aka sauya wa matsuguni na tsawon mako biyu kafin a yi maganin berayen, BBC ta ruwaito.

Berayen sun yi barna sosai inda suka lalata gidan yarin da kuma cin wayar wuta.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC

Kamar almara: Beraye sun fatattaki wasu fursunoni da ma'aikata daga wani gidan yari
Berayen da suka addabi gidan yari a Australia | Hoto: theguardian.com
Asali: UGC

Yankin ya dade yana fama da matsalar beraye, wannan kuma ya sa za a rage yawan mazauna gidan yarin zuwa tsawon wata hudu.

Kwamishinan kula da fursunoni na NSW, Peter Severin, ya ce za a rage ayyukan a kurkukun ne don magance barnar berayen kuma an dakatar da ziyarar cikin-gida har sai aikin gyaran ya kammala.

A ranar Talata, Mista Severin ya ce:

"Lafiya, aminci da walwala na ma'aikata da fursunonin shine babban fifiko na farko saboda haka yana da mahimmanci a garemu muyi aiki a yanzu don aiwatar da gyara."
"Muna bukatar daukar wannan matakin a yanzu don tabbatar da tsaftace gidan da kuma gyara kayayyakin more rayuwa."

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Bayan ritaya, an tura burutai wata kasa a matsayin ambasada

Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

A wani labarin, Rahoton da Legit.ng Hausa ta nakalto daga BBC ya bayyana cewa, Isra’ila ta shiga damuwa kan zaben Ebrahim Raisi a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Isra’ila, Lior Haiat, ya ce Mista Raisi shi ne shugaban kasar Iran mafi tsaurin ra’ayi da aka taba yi a tarihi.

Ya yi gargadin cewa shugaban zai ci gaba da inganta ayyukan nukiliyar kasar Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.