Da dumi-dumi: Shahararren sanatan PDP ya kayar da EFCC a kotu, ya yi nasara a karar da aka shigar

Da dumi-dumi: Shahararren sanatan PDP ya kayar da EFCC a kotu, ya yi nasara a karar da aka shigar

  • Sanata Peter Nwaoboshi ya sami gagarumar nasara a kan EFCC a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas
  • A yayin sauraron karar da mai shari’a Chukwujekwu Aneke ya jagoranta, kotun ta yanke hukuncin cewa karar da hukumar ta shigar ba ta da fa'ida
  • Kotun ta bayyana cewa hukumar ta gaza wajen tabbatar da cewa dan majalisar na PDP yana da laifi kan tuhumar da ta yi masa

Shekaru uku bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta zarge shi da yin sama da fadi da Naira miliyan 322, Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta saki Sanata Peter Nwaoboshi, a ranar Juma'a, 18 ga Yuni, kuma ta wanke shi daga tuhumar da ake masa.

Da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke ya ce hukumar ba ta tabbatar da hujjoji na laifukan da ta tuhumi Nwaoboshi ba, ya kara da cewa ba a kira shaidu don bayar da shaida ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana matsayarsa game da tsayawa takarar siyasa a Najeriya

Shahararren sanatan PDP ya kayar da EFCC a kotu, ya yi nasara a karar da aka shigar
Sanata Peter Nwaoboshi ya yi nasara a kotu kan shari'arsa da EFCC Hoto: Sen Peter Nwaoboshi
Asali: Facebook

A kan haka ne, Mai Shari’a Aneke ya kuma sallami kamfanoni biyu na Nwaoboshi - Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Sake Gurfanar da Orji Kalu

A gefe guda, Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.

Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel