Masu garkuwa da mutane 3 da ke shiga irin ta NDLEA sun faɗa komar 'yan sanda a Jigawa

Masu garkuwa da mutane 3 da ke shiga irin ta NDLEA sun faɗa komar 'yan sanda a Jigawa

  • Yan sanda a jihar Jigawa sun kama mutane uku da ake zargi da garkuwa da mutane ta hanyar amfani da kayan jami'an NDLEA
  • Wadanda aka kama sune Mujahid Muhammad, 30; Shahid Ibrahim, 20; and Haidar Muhammad-Kabir, 23, duk mazauna GRA Quaters
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu ya ce an fara bincike don gano sauran yan uwansu da masu sayar musu da makamai

Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Hadejia a jihar, The Cable ta ruwaito.

Today Ng ta ruwaito cewa kakakin yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suka yi yunkurin sace wani Cyprian Okechukwu a ranar 31 ga watan Mayu.

Taswirar Jihar Jigawa
Taswirar Jihar Jigawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa wadanda ake zargin sunyi bata kama ne da kayan jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sannan suka yi yunkurin tafiya da wanda abin ya faru da shi zuwa ofishinsu.

DUBA WANNAN: Bikin karɓar gwamnan PDP: APC ta bada kwangilar siyan tsintsiya miliyan uku

Sanarwar da rundunar yan sanda ta fitar game da yunkurin garkuwar

"A ranar 31 ga watan Mayu misalin karfe 1 na dare wani Cyprian Okechukwu ya shigar da rahoto a ofishin yan sanda da ke Hadejia da misalin karfe 8 na daren ranar, cewa wasu bata gari su uku cikin mota kirar Volkswagen Golf mai launin kore, sun zo gidansa, sanya da kayan NDLEA, sun yi kokarin kai shi ofishinsu da karfi da yaji.
"Wanda abin ya faru da shi ya lura cewa suna rike da bindiga pistol ce irin ta gargajiya wacce bata yi kama da irin na gwamnati ba.
"Hakan yasa ya ki yarda su tafi da shi mutane suka ji hayaniyar suka kawo masa dauki.
"Nan take aka ci galaba kan wadanda ake zargin aka kwace bindigan amma sun tsere," in ji shi.

KU KARANTA: Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

Yadda asirinsu ya tonu

Shiisu ya kara da cewa daya daga cikin makwabtan wanda abin ya faru da shi ya ce wadanda ake zargin sun taba zuwa gidan suna tambayar wanda abin ya faru da shi.

Shiisu ya ce daga bisani an kama mutum uku da ake zargi: Mujahid Muhammad, 30; Shahid Ibrahim, 20; and Haidar Muhammad-Kabir, 23, duk mazauna GRA Quaters da taimakon kwatancen da wanda abin ya faru da shi ya bada.

"Kazalika, an gano motar da aka kwatanta a hannunsu," in ji shi.

Kakakin yan sandan ya ce ana cigaba da bincike don gano sauran abokansu da masu sayar musu da makamai.

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164