Babbar Magana: Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook
- Wani fitaccen malamin addinin musulunci yace haramun ne amfani da alamar dariya a facebook domin muzgunawa wani
- Malamin mai amfani da suna ɗaya, Ahmadullah, yana da tarin mabiya a kafafen sada zumunta
- Yace babu laifi amfani da alamar wajen yin wasa, amma yace musulmai su guji bata ran yan uwansu
Wani babban malamin addinin musulunci a ƙasar Bangaladesh yayi wata sabuwar fatawa dake nuna haramcin amfani da alamar dariya a Facebook, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin wanda yake da tarin mabiya a dandalin sada zumunta yace haramun ne yin amfani da alamar dariya (Emoji) domin muzanta wasu.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sanatoci Zasu Bayyana Sunayen Ma'aikatu, Hukumomin da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati
Shahararren malamin mai suna, Ahmadullah, yana da mabiya aƙalla miliyan uku a facebook da kuma Youtube, sannan yana yawan gabatar da wa'azi a kafafen talabijin.
BBC ta ruwaito cewa, a cikin fatawar da ya wallafa a shafinsa, Ahmadullah, yayi bayani kan yadda ake cin mutuncin mutane a kafar sada zumunta na Facebook, kuma ta hanyar amfani da waɗannan alamomi.
Daga cikin bayanan malamin, yace:
"A zamanin yanzun mutane na amfani da alamar dariya (Emoji) a facebook domin zolayar yan uwansu."
"Idan kuka yi amfani da alamar dariya don izgilanci ga wani da yayi tsokaci a kafar sada zumunta,to kun aikata haramun a Musulunci."
Babu laifi amfani da alamar dariya domin yin wasa, inji malamin
Ahmadullah ya ƙara da cewa babu laifi musulmi yayi amfani da alamar dariya domin wasa ga yan uwansa.
Yace: "Idan mun yi amfani da alamar dariya da nufin wasa daidai da niyyar wadda ya wallafa wani saƙo, to wannan ba laifi ba ne."
KARANTA ANAN: Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace
Fitaccen malamin yayi kira da a gujewa amfani da alamar dariya da nufin ɓatawa wani rai, yace babu kyau bata ran musulmi har yakai ga faɗin wasu kalamai mara kyau.
A wani labarin kuma Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Ƙarasa Wani Muhimmin Aiki da Kwankwaso Ya Gaza
Gwamnan Kano, Ganduje, ya yi alƙawarin ƙarasa wani aikin hanya da tsohuwar gwamnati ta fara a jihar.
Ganduje yace ya umarci kwamishinan ayyuka ya binciko kundin aikin ya gano me yafaru ba'a kammala ba.
Asali: Legit.ng