Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Ƙarasa Wani Muhimmin Aiki da Kwankwaso Ya Gaza
- Gwamnan Kano, Ganduje, ya yi alƙawarin ƙarasa wani aikin hanya da tsohuwar gwamnati ta fara a jihar
- Ganduje yace ya umarci kwamishinan ayyuka ya binciko kundin aikin ya gano me yafaru ba'a kammala ba
- Ganduje ya baiwa al'umar jihar tabbacin daga yanzun duk wata bolar jihar za'a sarrafata ta zama wani abun amfani
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ranar Talata, ya sha alwashin ƙarasa aikin hanyar Gorondutse – Jakara wadda tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ya fara, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo
Hanyar wadda ta taso daga Gorondutse/Aminu Kano zuwa jakara an raɗa mata suna 'Sheikh Mahmud Salga' kuma gwamnatin tsohon gwamna, Rabi'u Kwankwaso ce ta fara aikin a zangon mulki na biyu.
Ganduje ya ɗauki wannan alƙawari ne yayin buɗe biki da aka yi wa take da 'Makon tsaftace jihar Kano' a Jakara.
Bayan Gwamnan ya bayyana muhimmancin hanyar, ya nuna buƙatar kammala aikin cikin gaggawa.
Yace: "Wannan hanyar mai muhimmanci da aka bar mana, nayi alƙawarin ƙarasa ta cikin ƙanƙanin lokaci."
"Na riga na umarci kwamishinan ayyuka ya koma ofishinsa ya kakkaɓe kundin aikin hanyar, ya gano mana me yasa ba'a kammala ba."
"Amma ina tabbatar muku da cewa gwamnatin mu zata yi duk me yuwu wa a ƙarasa aikin hanyar."
KARANTA ANAN: Wata Jami'a Ta Kori Ɗalibi Ɗan '500-Level' Saboda Ya Soki Gwamna a Facebook
Gwamnatin Kano ta haɗa hannu da wasu kamfanoni
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta haɗa hannu da wani kamfani mai zaman kansa domin sarrafa bolar jihar Kano zuwa abun amfani.
Yace: "Kamar yadda muka gabatar da aikin shekara 2 da suka gabata, gashi yau mun ƙaddamar da shi. Ina mai tabbatar wa jama'ar jihar Kano cewa daga yanzun bola zata fara zama abin amfani."
A wani labarin kuma Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari
Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci.
Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng