Wani Kwamishina Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Bayyana Ranar Hutu Saboda Jimami

Wani Kwamishina Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Bayyana Ranar Hutu Saboda Jimami

  • Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya rasa ɗaya daga cikin kwamishinoninsa sanadiyyar hatsarin mota
  • Gwamnan yayi takaicin rasuwar kwamishinan, inda ya bayyana shi a matsayin ginshiƙin gwamnatinsa
  • Ya kuma bayyana ranar hutu a faɗin jihar domin girmama marigayi, Fidelis Nweze

Kwamishinan kula kayayyakin gwamnati na jihar Ebonyi, Fidelis Nweze, ya rigamu gidan gaskiya sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da shi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahoton vanguard ya nuna cewa, Kwamishinan ya mutu ne a asibitin Turkish dake Abuja bayan an samu nasarar yi masa aiki.

KARANTA ANAN: Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Ƙarisa Wani Muhimmin Aiki da Kwankwaso Ya Gaza

Marigayi Nweze, na kan hanyarsa ta zuwa Enugu ranar Asabar lokacin da hatsarin ya rutsa da shi a hanyar Eke Obinagu, ƙaramar hukumar Enugu ta arewa da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

Kwamishina Nweze
Wani Kwamishina Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Bayyana Ranar Hutu Saboda Jimami Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A halin yanzun direban da ya tuƙa Mr. Nweze a wannan loƙacin yana kwance a asibiti yaji raunuka da dama.

KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo

Gwamna Umahi yayi alhinin mutuwar Nweze, ya bayyana Laraba ranar hutu

A wani jawabi da Gwamna Umahi yayi wa manema labaran gidan gwamnati cikin damuwa da rawar murya, ya bayyana marigayin a matsayin ɗan uwa, da kuma aboki.

Yace: "Nweze ya mutu da misalin ƙarfe 9:15 na safe a asibitin Turkish, Abuja. Na yi matuƙar baƙin ciki saboda yana daga cikin ginshiƙan wannan gwamnatin."

"A wuri na, Nweze ɗan uwa ne, kuma aboki na ne wanda ya yi tafiyar da ba zai dawo ba. Mun yi iya bakin ƙoƙarin mu, babu aiki Ranar Laraba saboda alhinin mutuwar Nweze."

A wani labarin kuma Wata Jami'a Ta Kori Ɗalibi Ɗan '500-Level' Saboda Ya Soki Gwamna a Facebook

Jami'ar jihar Akwa Ibom ta sallami ɗalibinta dake shekarar ƙarshe saboda zargin ya ɓata wa gwamnan jihar suna.

Ɗaliɓin mai suna, Iniobong Ekpo, yayi rubutun zargi a kan gwamnan jihar a dandalin sada zumunta tun shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel