Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari

Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari

  • Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce imanin da tayi da matasan kasar nan yana nan daram
  • Kamar yadda Aisha Buhari ta bakin wacce ta wakilceta, Dr Rukayya Gurin ta sanar, tana jin dadin goyon bayan mulkin Buhari da ake
  • Ta tabbatar wa da matasa da mata cewa itama tana goyon bayan su dari bisa dari

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari a ranar Litinin ta ce imanin da tayi da matasa da mata a Najeriya har yanzu yana nan daram.

Matar shugaban kasan ta sanar da haka ne a taron farko na matasan jam'iyyar APC da aka yi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: 2023: Manyan matsaloli 7 dake barazanar hargitsa APC a jihar Kano

Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari
Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya

Wakiliyar Aisha Buhari ce ta halarci taron

Ta samu wakilcin babbar mataimakiyarta a fannin harkokin mata da mulki, Dr Rukayyatu Gurin, wacce tace matar shugaban kasan na bayyana goyon bayanta da mayar da hankali a jam'iyyar.

Ta bayyana cewa akwai tabbacin taron zai samu abinda yayi niyya na wanzar da hadin kai da cigaba tsakanin 'yan APC, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Ina da tabbacin taron nan zai cimma nasarar da ake bukata.

"Imanin da nayi da matasa har yanzu yana nan daram. Ina godiya gareku da irin goyon bayan da kuke cigaba da bai wa gwamnatin Buhari.

"Ina tabbatar muku da goyon bayana dari bisa dari," tace.

A wani labari na daban, Alhaji Yusuf Galami, dan takarar jam'iyyar APC a zaben maye gurbi da aka yi domin cike kujerar majalisar tarayya ta mazabar Gwaram a jihar Jigawa ya samu nasara.

Farfesa Ahmad Shehu, baturen zaben, bayan tattara kuri'u daga akwatuna 248 ya bayyana Galambi a matsayin mai rinjaye da kuri'a 29,372 a kan Kamilu Inuwa na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 10,047.

"Bayan Galambi ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben maye gurbin, ya zama mai nasarar a zaben," Shehu ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Gwaram kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel