Masu jiran tarwatsewar kasar Najeriya zasu sha kunya, Yemi Osinbajo

Masu jiran tarwatsewar kasar Najeriya zasu sha kunya, Yemi Osinbajo

  • Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasan Najeriya yace masu jiran watsewar kasar nan zasu sha kunya
  • Ya sanar da cewa yadda ake kai hade kuma tsintsiya daya yafi zama alheri da kuma cigaba a kowanne bangare na kasar nan
  • Osinbajo yace akwai tabbacin cewa matasan APC ba zasu zuba ido su ga kasar Najeriya ta tarwatse ba

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbaji ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya zata cigaba da zama kai hade a matsayin kasa daya duk da masu son ganin rabuwarta.

Ya sanar da haka a ranar Litinin a Abuja yayin taron farko na matasan jam'iyyar APC, Channels TV ta ruwaito.

"A bangaren son kawo hargitsi da rabewar kai, zan iya cewa mun fi karfi idan muna tare kuma a ganin duk masu fatan ganin rabewar kasar nan, basu kyauta ba," Farfesa Osinbajo ya sanar da taron matasa da masu ruwa da tsaki na APC.

KU KARANTA: Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniy

Masu jiran tarwatsewar kasar Najeriya zasu sha kunya, Yemi Osinbajo
Masu jiran tarwatsewar kasar Najeriya zasu sha kunya, Yemi Osinbajo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace

Ya kara da cewa, "Yawanmu yana da matukar amfani ko a fannin tattalin arziki. Jama'armu zasu fi samun abinda ya dace idan muna da yawa a kasar nan. Kamar yadda sauran manyan kasashe suke, abinda muka saka gaba shine tabbatar da wannan hadaka tayi, kowa ya dinga ji ana yi da shi.

"Duk masu jira a gefe, ganin cewa wannan babbar kasar Najeriya za ta rabu domin su kwashi rabonsu, zasu sha kunya kuma ina da tabbacin duk wanda yake nan zai tabbatar da hakan bata faru ba."

Mataimakin shugaban kasan ya tabbatar da cewa akwai bukatar kowannen dan Najeriya ya zamo yana da dama ta inganta halin da yake ciki kuma yayi kira ga matasa da su shiga al'amuran kasar nan.

Yayi kira ga masu tasowa da kada suce lokacinsu yayi don hakan manya su matsa su basu wuri, hakan ba dole ta iya faruwa ba, Channels TV ta wallafa.

A wani labari na daban, mambobin kungiyar IPOB suna da wata yarjejeniya tsakaninsu da masu rajin raba kasar Kamaru a wasu fannoni na horarwa da kuma musayar makamai, Daily Trust ta tabbatar da hakan daga wata majiyar tsaro mai karfi.

Duk da har yanzu yanayin hadin kansu bai fito fili ba, bincike ya nuna cewa wani bangare na kasar Kamaru masu yaren Turanci kuma inda masu son kafa kasa Ambazonia suke suna iya shigowa Najeriya hankali kwance ta jihar Cross River wadanda suke da al'adu masu kamanni.

A yayin da IPOB ke yakar hukumomin tsaron Najeriya domin kafa jamhuriyar Biafra, masu neman yancin kai na Ambazonia suna bukatar a raba kasar Kamaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng