Shugabannin kudu da na arewa sun yabawa gwamnonin kudu bisa tir da IPOB

Shugabannin kudu da na arewa sun yabawa gwamnonin kudu bisa tir da IPOB

  • Shugabannin Arewa da Kudancin Najeriya sun yabawa gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya
  • Sun yaba musu ne bisa barranta da yunkurin da IPOB ke yi na ballewa daga Najeriya domin kafa Biafra
  • Shugabannin na kudu sun nemi gwamnonin Arewacin Najeriya da su ba jama'ar Ibo dake zaune a Arewa kariya

Shugabannin arewa da kudancin Najeriya a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuni sun goyi bayan matsayar gwamnonin kudu maso gabas da sauran shugabanni a yankin Ibo bisa nacewa kan hada kan kasa tare da nesanta yankin da kiraye-kirayen ballewa daga IPOB.

Da take bayyana goyon baya ga matsayar shugabannin kudu maso gabas, kungiyar koli ta zamantakewar arewa, Arewa Consultative Forum (ACF), da takwararta a shiyyar kudu maso kudu, kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) ta ce Najeriya ta fi kyau a dunkule uwa daya.

KU KARANTA: Hotunan yadda jama'ar Zaria suka yi wa 'yan bindiga sallar Al-Qunuti

Kun kyauta: Dattawan kudu da arewa sun yabawa 'gwamnonin kudu bisa barranta da IPOB
Wasu daga cikin tsagerun IPOB dake zanga-zanga | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kakakin ACF, Mista Emmanuel Yawe, ya shaida wa jaridar Leadership cewa:

"Idan akwai wata kabila da ta ci gajiyar hadin kan Najeriya, to 'yan kabilar Ibo ne. Idan suka jagoranci ballewar Najeriya, za su haifar da kiyayya mai yawa daga wadanda suke kaunar Najeriya kuma suke son ta ci gaba da kasancewa a dunkule. Dole ne su tafi.”

A nata bangaren, PANDEF ta ce ta goyi bayan kudurin gwamnonin kudu maso gabas da shugabanni don yin tir da ayyukan 'yan ta'addan IPOB.

Kakakin PANDEF, Hon Ken Robinson, ya ce:

“Kada a ga laifin matsayin shugabannin siyasa a kudu maso gabas. Mun yarda cewa akwai wasu yanayi a kasar da za a iya kaucewa kwata-kwata, nuna wariya, son zuciya, da rashin adalci, yana da kyau amma ba ma tunanin, a matsayinmu na shugabanni, cewa rabuwa shine mafita."

Gwamnonin kudu maso gabas na neman kariya ga Ibo mazauna yankin Arewa

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa gwamnonin kudu maso gabas sun yi kira ga gwamnonin arewa da sauran su da su kare mutanensu da ke zaune a arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, Engr David Umahi ya yi kiran nan da nan bayan taron shugabannin kudu maso gabas da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga Yuni a jihar Enugu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shuwagabannin kudu maso gabas sun barranta da yunkurin ballewar kungiyar IPOB da wasu masu neman kafa kasar Biafra, suna masu cewa kungiyoyin basa magana a madadin kabilar Ibo.

Shugabannin wadanda suka hada da gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya, dattawa, shugabannin gargajiya da shugabannin addinai a yankin, sun tabbatar da aniyarsu ta dunkulewar Najeriya.

An yanke shawarar ne bayan taron sirri na tsaro a gidan gwamnatin jihar Enugu.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Bayan Shekaru 6, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC

Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa

A wani labarin, Chris Ngige, Ministan kwadago, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karbar tattaunawa don magance rikicin dake faruwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, The Nation ta rahoto.

A kwanakin baya kada, an yi ta kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati a duk fadin kudu maso gabashin kasar, lamarin da ya kai ga kashe jami'an tsaro da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel