Ba sauran bin dogon layi: INEC ta saukaka hanyar yin rajistar masu zabe

Ba sauran bin dogon layi: INEC ta saukaka hanyar yin rajistar masu zabe

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da sabuwar sanarwa kan rajistar zabe a Najeriya
  • Hukumar ta ce ta samar da sabuwar hanyar yin rajista ba tare da bin dogon layin rajista ba
  • Ta ce za a fara rajistar zaben ne ta yanar gizo domin rage cunkoso da yawatar layi a cibiyoyin rajista

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a kokarinta na Ci gaba da Ilimantar da Masu Zabe a mako mai zuwa, ta bullo da wata hanyar shiga yanar gizo don yin rajista.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Litinin a Abuja, jaridar Punch ta ruwaito.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata mai taken “Ci gaba da Rajistar Masu Zabe: Kwararru a kafafen yada labarai, INEC sun amince su wayar da kan 'yan kasa,” Shugaban ya ce rajistar ta yanar gizo za ta taimaka wajen rage dawainiyar dogayen layuka a lokacin shirin CVR.

KU KARANTA: Kamfanin MTN Zai Tattara Komai Nashi Ya Fice Daga Najeriya Saboda Wasu Dalilai

Ba sauran dogon layi: INEC ta saukaka hanyar yin rajistar masu zabe
Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) | Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Ya ce:

“A mako mai zuwa, Litinin 28 ga Yuni 2021, Hukumar za ta ci gaba da Rijistar Masu Zabe a duk fadin kasar.
"A yayin yin haka, Hukumar na gabatar da wata hanyar da za ta baiwa 'yan Najeriya da suka cancanta damar fara rajistar a matsayin masu jefa kuri'a ta yanar gizo kafin kammala aiki a cibiyoyin da aka ware a fadin kasar"
"Wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da wani babban aiki na amfani da hanyar yanar gizo, wanda yake daidai da kudurin hukumar na ci gaba da zurfafa amfani da fasaha a harkar zabe a Najeriya.
"Kamar dai yadda aka fadada damar yin amfani da runfunan jefa kuri'a a Kananan Hukumomin, hukumar tana kira ga kafofin yada labarai don tallafawa domin wannan sabon tunanin ya zama ya yi nasara."

Jaridar Today ta ruwaito shugaban na INEC yayin da yake magana a kan tsawon wa'adin ci gaba da rajistar, in da ya bayyana karara cewa, aikin zai kasance na tsawon shekara guda.

Ya kara da cewa:

“Nasarar wannan aikin ya dogara ne, da mahimmin matakai na wayar da kan 'yan kasa ta hanyar ilimantar da masu jefa kuri’a.
"Za a samu sabbin masu rajista, da bukatar neman canjin jihohi da tsakanin jihohi da kuma sauya katunan masu zabe kamar yadda doka ta tanada."

KU KARANTA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa

Cikakken Bayani: INEC Ta Bayyana Sabon Adadin Runfunan Zaɓe a Najeriya, Ta Soke Wasu 746

A wani labarin, Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta soke wasu runfunan zaɓe 746 dake faɗin Najeriya, waɗanda mafi yawancin su a wurin bauta, gidan sarauta da kuma wuri mai zaman kanshi suke, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya faɗi haka ranar Laraba a Abuja, a wurin taron da hukumar ke gudanarwa da kwamishinonin zaɓe RECs.

Asali: Legit.ng

Online view pixel