Gwamnatin Buhari ta fadi dalilan da yasa ba za ta amince da ci gaban Twitter ba

Gwamnatin Buhari ta fadi dalilan da yasa ba za ta amince da ci gaban Twitter ba

  • Gwamnatin Buhari ta ce sam kamfanin Twitter da ma bai da rajistar da ta dace ya yi ayyukansa a Najeriya
  • Gwamnatin Buhari ta ce ba za ta amince kamfanin ya ci gaba da ayyukansa ba har sai ya yi rajista
  • Hakazalika shugaba Buhari ya bada umarnin a zauna da kamfanin na Twitter don tattauna batunsa

Gwamnatin tarayya ta ce ba a halatta ayyukan Twitter a jerin kafafen sada zumunta na Najeriya ba, The Cable ta ruwaito.

Ta ce ana amfani da Twitter wajen yada labarai "wadanda ke jefa rayuwar 'yan Najeriya cikin hadari da kuma haifar da rashin hadin kai a kasar."

Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu, ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya bayyana a gaban majalisar wakilai bisa bincike kan lamarin Twitter.

KU KARANTA: Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar dokoki ta kasa

Gwamnatin Buhari ta fadi dalilan da yasa ba za ta amince da ci gaban Twitter ba
Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Biyo bayan dakatar da ayyukan shafin Twitter a kasar, majalisar wakilai ta umarci kwamitocinsa na sadarwa, adalci, bayanai da al'adu, da tsaron kasa da kuma leken asiri na kasa da su binciko yanayin da ya sa aka yanke hukuncin.

Da yake magana a wajen binciken a ranar Talata, Lai Mohammed ya ce Dokar Kamfanoni da Kawance ta shekarar 2020 ba ta yarda kamfanonin kasashen waje su yi kasuwanci a Najeriya ba idan ba su yi rajista ba.

Saboda haka ya ce ba za a bai wa Twitter "halaccin hakkoki" na yin aiki ba har sai ya yi rajista a Najeriya karkashin dokar ta kamfanoni da kawance.

Shugaba Buhari ya amince a zauna da jami'an Twitter don sasanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Babatunde Fashola, Ministan Ayyuka da Gidaje da Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya, da su tattauna da Twitter game da haramcin shafin na sada zumunta.

Bayan Fashola da Malami, sauran ministocin sun hada da Dr Isa Pantami (Sadarwa da Tattalin Arziki), Chris Ngige, (Kwadago), da Geoffrey Onyeama (Harkokin Waje), Daily Trust ta rahoto.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da rukunin tawagar Gwamnatin Tarayya da za ta zauna tare da Twitter kan dakatarwar da aka yi mata na ayyukan sada zumunta a Najeriya kwanan nan."

KU KARANTA: Ba sauran bin dogon layi: INEC ta saukaka hanyar yin rajistar masu zabe

A wani labarin, Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana cewa kamfanin twitter ya taka rawar bayan fage akan babbar zanga-zangar #EndSARS da aka yi shekarar da ta gabata, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a wurin binciken dokar hana twitter da kwamitocin majalisar wakilai da suka haɗa da, kwamitin labarai, ICT da shari'a ke gudanarwa.

Mr. Muhammed yace:

"Kamfanin twitter ya haɗa wa masu zanga-zangar #EndSARS kuɗi, kafin daga bisani a karkatar da su ta wata hanyar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel