Kotun Najeriya ta yanke wa wani dan bautar kasa zaman gidan yari, ta ba da dalilin hukuncin

Kotun Najeriya ta yanke wa wani dan bautar kasa zaman gidan yari, ta ba da dalilin hukuncin

  • Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa na ci gaba da yin hukunci a kan masu damfarar intanet a kasar
  • Na baya-bayan nan, hukumar yaki da rashawar ta tabbatar da hukunta wani dan bautar kasa bayan ta gabatar da hujjar cewa ya aikata zamba
  • Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, ya yi alkawarin cewa hukumar za ta gurfanar da duk wanda aka samu da laifi ba tare da la’akari da matsayinsa ba

Babban Kotun jihar Kwara da ke zaune a Ilorin ta yanke wa wani dan bautar kasa (NYSC) da ke hidimar kasa a Ibadan, jihar Oyo, Caleb Oyeyemi, hukuncin daurin shekaru biyu a kan damfara ta soyayya.

Mai shari’a Adenike Akinpelu ce ta yanke wannan hukunci bayan kotu ta samu Oyeyemi da laifi kan tuhume-tuhume biyu da hukumar yaki da rashawa ke yi masa, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojoji

Kotun Najeriya ta yanke wa wani dan bautar kasa zaman gidan yari, ta ba da dalilin hukuncin
NYSC ta sha shawartan yan bautan kasa da su zamo masu da'a Hoto: National Youth Service Corps - NYSC
Asali: Facebook

Kotun ta yanke wa dan bautar kasan hukuncin daurin shekara guda a kan kowane laifi, wadanda za su yi aiki a lokaci daya.

An ba shi zaɓin biyan tara

Sai dai kuma, alkalin, ya ba shi zabin biyan tarar N200, 000 a kan kowane kara.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa EFCC ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 16 ga Maris, 2020, bisa rahoton sirri.

An gurfanar da shi a ranar 26 ga Nuwamba, 2020, kuma ya amsa laifinsa lokacin da aka karanta masa su.

Ana Iya Tura Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Filin Daga Suyi Yaƙi, Shugaban NYSC

A wani labarin, shugaban hukumar NYSC na masu yan yi wa kasa hidima, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce masu yi wa kasa hidimar suna cikin jami'an tsaron Nigeria kuma ana iya basu horon zuwa yaki idan bukatar hakan ta taso.

The Nation ta ruwaito cewa Ibrahim ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da aka yi da shi a ranar Laraba yayin da ya ke magana kan batun kiraye-kirayen da wasu ke yi na cewa a soke tsarin yi wa kasa hidimar.

Ya bayyana cewa irin horaswar da aka bawa masu yi wa kasa hidimar na makonni uku na shirya su tamkar sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel