Tsohon tauraron Manchester United ya ziyarci gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

Tsohon tauraron Manchester United ya ziyarci gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

  • Odion Ighalo ya shiga cikin jerin 'yan wasan kwallon kafar Najeriya na da da na yanzu wadanda suka kai ziyarar girmamawa ga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
  • Ziyarar Ighalo na zuwa ne kwanaki kadan bayan tsohon kyaftin din Super Eagles Mikel Obi da Kelechi Iheanacho sun gana da dan siyasan
  • Dan wasan na Al-Shabab na Saudiyya ya gode wa gwamnan kan irin tarbar da ya yi masa a watan Maris tare da rokon sauran da su yi koyi da shi

Tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya Odion Ighalo ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gidansa da ke Abuja.

Gwamnan na jihar Kogi ya ci gaba da tarbar ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya na da da na yanzu a makonnin da suka gabata, kuma Ighalo ya kai ziyarar ne a ranar Litinin, 21 ga Yuni.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun damke wani da ake zargin ‘dan fashi ne da ke tserewa zuwa jihar Oyo da kayan sojoji da layoyi

Tsohon tauraron Manchester United ya ziyarci gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello
Odion Ighalo ya ziyarci Gwamna Yahaya Bello Hoto: Soccernet
Asali: UGC

Tsohon dan wasan na Watford na Ingila ya kai ziyarar ne yan kwanaki bayan tsohon kyaftin din Super Eagles John Mikel Obi da dan wasan gaban Leicester City Kelechi Iheanacho sun gana da gwamnan na jihar Kogi.

A cikin jawabin nasa, rahotanni sun ce Ighalo ya bayyana gwamnan a matsayin ‘mai dinke baraka,’ ya kara da cewa salon shugabancinsa shine ginshikin fata mai kyau ga matasa a Najeriya.

Dan wasan na Al-Shabab na Saudiyya ya gode wa gwamnan kan tarbar da ya yi wa tsoffin 'yan wasan Najeriya a watan Maris, yayin da ya bukaci sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da halayen jagoranci na Bello.

A wani labarin na daban, fitaccen dan wasan kwallon kafa Ahmed Musa ya nuna damuwarsa da rashin jin dadinsa a kan mummunan lamarin da ya faru a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna a ranakun karshen mako.

Kano Pillars sun karba bakuncin Akwa United a wani wasa da manyan kungiyoyin kwallon kafan suka yi.

Amma kuma magoya bayan Kano Pillars sun kutsa filin wasa a fusace domin lakadawa alkalan wasa duka bayan sun soke kwallon da ta shiga raga a minti na 85 na wasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel