Da duminsa: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya

Da duminsa: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya

- Bayan musayar yawu a teburin sulhu, an cima matsaya tsakanin gwamnatin Kaduna da NLC

- Gwamnan jihar ya jaddada cewa lallai sai ya sallami ma'aikata

- Kungiyar Kwadago kuma tace wajibi ne sai ya biwa ma'aikata hakkinsu

Gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon Najeriya NLC sun yi yarjejeniya kan shirin sallamar ma'aikata kimanin 7000 da gwamnatin El-Rufa'i ke shirin yi.

Tun ranar Litnin NLC ta fara zanga-zanga da yajin aiki kan abinda gwamnatin jihar tayi.

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta shirya zaman sulhu tsakanin bangarorin biyu a Abuja.

PT ta rahoto cewa daga cikin yarjejeniyar da sukayi shine gwamnatin Kaduna ta cigaba da muradinta amma ta bi dokokin kwadago na korar ma'aikata bisa sashe na 20 na dokar kwadago.

Hakazalika sun yarje cewa NLC ba zata cigaba da yajin aikin ba amma kuma kada gwamnatin jihar ta hukunta duk wani ma'aikacin gwamnatin jihar da ya shiga yajin aikin.

Zaku tuna cewa gwamnatin Kaduna ta sanar da sallamar malaman jinya da malaman jami'ar KASU da suka shiga yajin aikin. Wannan yarjejeniyar ta rusa wannan hukunci.

KU KARANTA: Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci

Da duminsa: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya
Da duminsa: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya Hoto: @el-rufa'i
Asali: UGC

DUBA NAN: Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

Bayan haka an kafa kwamitin mutum 10; mutum 6 daga bangaren gwamnatin Kaduna, 3 daga bangaren NLC, da kuma mutum 1 daga bangaren gwamnatin tarayya domin tattauna yadda za'a wanzar da yarejejeniyar.

Dukkan bangarorin biyu sun rattafa hannu kan wannan yarjejeniya.

A wani labarin daban, Ofishin Farai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Alhamis ta sanar da tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin da ta kwashe kwanaki 11 tana yi da kungiyar Hamas a zirin Gaza.

Sanarwar ta ce tawagar ofishinsa na bangaren tsaro ta amince da bukatar da sulhu da kasar Egypt za ta yi tsakanin bangarorin biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel