Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojoji
- Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban hafsan sojin kasa
- An tabbatar da Yahaya ne a zaman majalisa da aka yi a yau Talata, 22 ga watan Yuni bayan rahoton kwamitin soji
- Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin tsaro, Sanata Aliyu Wamakko ne ya gabatar da rahoton
Majalisar dattijai a ranar Talata ta tabbatar da nadin Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji (COAS), jaridar Vanguard ta ruwaito.
Tabbatar da Yahaya ya biyo bayan gabatarwa da kuma duba rahoton kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai kan tsaro da sojoji a zaman majalisa.
KU KARANTA KUMA: Tsohon tauraron Manchester United ya ziyarci gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello
Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin tsaro, Sanata Aliyu Wamakko ne ya gabatar da rahoton, jaridar The Nation ta ruwaito .
Janar Yahaya ya kasance yana aiki a matsayin shugaban soji na rikon kwarya bayan rasuwar magabacinsa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya mutu a hatsarin jirgin saman soja a Kaduna.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sun damke wani da ake zargin ‘dan fashi ne da ke tserewa zuwa jihar Oyo da kayan sojoji da layoyi
Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya
Farouk Yahaya, shugaban rundunar sojin kasa ya ce yana da gogewar da zai iya shawo kan matsalar tsaron kasar nan.
Yahaya ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da lamurran tsaro domin tantancewa.
Shugaban sojin ya ce ya halarci yaki da kwantar da tarzoma a Liberia inda ya kara da cewa gogewarsa kadai ta isa ta inganta tsaron kasar nan, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng