Bangarori biyu na jam'iyyar APC sun yi rikici, an harbi mutum biyu wasu da dama sun jikkata

Bangarori biyu na jam'iyyar APC sun yi rikici, an harbi mutum biyu wasu da dama sun jikkata

  • Magoya bayan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) biyu a Offa, jihar Kwara sun yi fada a ranar Lahadi 20 ga watan Yuni
  • Mutane biyu sun samu raunin bindiga yayin rikicin da magoya bayan jam'iyyar biyu suka yi an kuma kai su asibitoci daban-daban
  • Ana zargin wadanda suka yi rikicin magoya bayan Sanata Lola Ashiru ne da abokin hammayarsa, Femi Agbaje, kwamishina a jihar

Bangarorin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) biyu a jihar Kwara sun yi mummnar fada a garin Offa a ranar Lahadi, rahoton Premium Times.

An yi rikicin ne tsakanin bangarori biyu na jam'iyyar - daya masu biyaya ga kwamishinan albarkatun ruwa, Femi Agbaje, dayan bangaren kuma masu goyon bayan sanata mai wakiltar Kwara ta Kudu, Lola Ashiru, dukkansu yan gari daya.

Tutar jam'iyyar APC
Tutar jam'iyyar All Progressive Congress, APC. Hoto: Today NG
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

Mr Agbaje, wanda ya fara zuwa kamfen a garin a makon da ta gabata, ya sake zuwa kamfen din a ranar Lahadi kafin a fara rikicin.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa bangarorin biyu sun tada rikici har da musayar wuta da bindigu, hakan yasa mutane da dama suka tsere domin tsira da ransu.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewa mutane biyu sun jikkata sakamakon harbinsu da bindiga aka yi an kuma garzaya da su asibiti.

Kamfen din sati-sati

Hadimin kwamishinan, Azeez Idowu, ya ce masu rike da mukaman siyasa a karamar hukumar Offa ne suka shirya kamfen din na sati-sati.

Ya ce an fara kamfen din ba tare da wata matsala ba tun ranar Lahadi 13 ga watan Yuni. Sai dai abubuwa sun tabarbare a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuni, a lokacin da wasu da ake zargin yan daba da yan siyasa suka dauki haya ne suka kai hari.

KU KARANTA: Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

Kafin fara kamfen din a mazabar, rahotanni sun ce Agbaje ya yi jefa wa Sanata Ashiru maganganu masu zafi duk da cewa bai ambaci sunansa ba yana cewa wasu 'sakarkaru' sun ba su goyon bayan kamfen din mu.

Yan siyasan biyu da ke rikici yan gari daya ne.

A wani labarin, wasu masu zanga-zanga a Umaru Yar'Adua Way, babban birnin tarayya Abuja, a safiyar ranar Litinin sun banka wuta a kan titi, hakan ya janyo cinkoson ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito.

Titin na Musa Yar'Adua Way ne ake bi idan za a tafi filin tashi da saukan jiragen sama a birnin tarayyar Abuja.

The Cable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar suna ta ihu cewa 'Buhari Must Go' ma'ana 'Dole Buhari Ya Tafi' yayin da suke dauke da takardu masu rubutu daban-daban na nuna rashin kaunar kasancewar shugaban kasar a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel