Cikakken Bayani: INEC Ta Bayyana Sabon Adadin Runfunan Zaɓe a Najeriya, Ta Soke Wasu 746

Cikakken Bayani: INEC Ta Bayyana Sabon Adadin Runfunan Zaɓe a Najeriya, Ta Soke Wasu 746

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta soke runfunan zaɓen dake masallatai da Coci-Coci
  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya faɗi haka ranar Laraba a babban birnin tarayya, Abuja
  • Yakubu yace an samu ƙarin wasu runfunan zaɓe saboda wata kwaskwarima da hukumar ta gudanar

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta soke wasu runfunan zaɓe 746 dake faɗin Najeriya, waɗanda mafi yawancin su a wurin bauta, gidan sarauta da kuma wuri mai zaman kanshi suke, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Ƙi Sakin Wani Basarake, Sun Saki Matansa Biyu Duk da An Basu Maƙudan Kuɗi

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya faɗi haka ranar Laraba a Abuja, a wurin taron da hukumar ke gudanarwa da kwamishinonin zaɓe RECs.

Shugaban Hukumar Zsɓe, Farfesa Mahmud Yakubu
Da Ɗumi-Ɗumi: INEC Ta Soke Wasu Runfunan Zaɓe 746 a Faɗin Najeriya Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

INEC ta bayyana adadin runfunan zaɓe a Najeriya bayan ta yi garambawul

Daga runfunan zaɓen 119, 973 da ake da su, Farfesa Yakubu yace yanzun akwai runfunan zaɓe 176, 846 a faɗin Najeriya, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban INEC ɗin yace an samu wannan ƙarin ne bayan wata kwaskwarima da hukumar ta gudanar a faɗin runfunan zaɓen dake ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

Yace: "Bayan tattaunawa da shawarwari da masu faɗa a ji da ma'aikatan mu suka yi, a halin yanzun ƙananan runfunan zaɓe 56,872 da muƙe da su a Najeriya an haɗa su da runfunan zaɓe 119,974."

"Hukumar zaɓe na farin cikin bayyana cewa tun sanda aka ƙirƙiri runfunan zaɓe shekara 25 da suka gabata a shekarar 1996, yanzun an samu nasarar ƙara yawan runfunan zaɓe masu zaman kansu. A halin yanzun Najeriya na da runfunan zaɓe 176,846."

A wani labarin kuma Abun Tausayi, Iyayen Ɗaliban Islamiyya da Aka Sace a Neja Sun Fara Bin Masallatai, Coci Suna Roƙon Kuɗi

Rahotanni sun bayyana cewa iyayen yaran sun fara neman tallafi a masallatai da coci-coci domin haɗa kuɗin da yan bindiga suka nemi a basu.

Shugaban makarantar ya sake magana da masu garkuwan, sun faɗa masa yaran sun fara kamuwa da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel