PDP ta gamu da kalubale tun kafin zaben Gwamna, ‘Dan takara ya kai Shugabannin jam'iyya kotu

PDP ta gamu da kalubale tun kafin zaben Gwamna, ‘Dan takara ya kai Shugabannin jam'iyya kotu

  • Mista Zeribe Ezeanuna ya tafi kotu a kan zaben Gwamnan jihar Anambra
  • ‘Dan jam’iyyar adawar ya soki kudin da ake karba kafin a yanki fam a PDP
  • Lauyan ‘dan siyasar ya kai Shugabannin PDP uku da hukumar INEC kotu

Daya daga cikin masu harin kujerar gwamnan jihar Anambra a karkashin PDP, Zeribe Ezeanuna, ya shigar da kara kotu, ya na tuhumar jam’iyyarsa.

Mista Zeribe Ezeanuna ya na zargin jam’iyyar PDP da cire shi daga cikin masu shiga zaben bana. Hakan ya sa ya bukaci a biya shi miliyoyi ya rage zafi.

Wadanda ake tuhuma a kotu

Jaridar Punch ta ce ‘dan siyasar ya hada shugaban PDP na kasa, Uche Secondus da hukumar zabe ta INEC, duk ya maka a gaban Alkali a Akwa Ibom.

KU KARANTA: APC za ta saye tsintsiyoyi miliyan uku domin tarbar sababbin 'Ya 'ya

Zeribe Ezeanuna ya ce hukumar INEC da shugabannin jam’iyyar PDP sun tursasa masa a kan sai ya biya N5m kafin ya shiga cikin masu neman takara.

Sauran wadanda Ezeanuna ya kai kara sun hada da sakataren gudanarwa na PDP, Austin Akobundu da shugaban jam’iyya na Anambra, Ndubuisi Nwobu.

Shari’a a kotun Awka, jihar Akwa Ibom

Yanzu wannan magana ta na gaban babban kotun tarayyar da ke garin Awka, inda Lauyoyin Ezeanuna suke so kowane wanda ake kara ya ba shi N50m.

Jezie Ekejiuba, wanda shi ne ya tsaya wa Mista Ezeanuna ya na neman N200m daga hannun Uche Secondus, Austin Akobundu, Ndubuisi Nwobu da INEC.

Zeribe Ezeanuna a taro
Mr. Zeribe Ezeanuna Hoto: www.sunnewsonline
Asali: UGC

KU KARANTA: Okorocha ya fadawa Ibo caca ce su biyewa kiran raba Najeriya

A wannan kara mai lamba ta FHC/AWK/CS/29/2021, The Nation ta ce Lauyan wanda ya shigar da karar ya na so a hana biyan wasu kudi kafin a iya neman takara.

Alkali Nnamdi Dimgba zai saurari wannan shari’a, inda zai warware gardama a game da wajabcin bada N5m a matsayin kudin shiga zaben fitar-da-gwani a PDP.

Lauyan ya na so Alkali ya taka wa jam’iyyar PDP burki a kokarin da ta ke yi na hana wanda yake wakilta a kotu, damar shiga neman tikitin gwamnan jihar Anambra.

A ranar Litinin ne ku ka samu rahoto cewa bayan tsawon watanni, ana shirin tsaida ranar gudanar da babban gangamin APC inda za a zabi sababbin shugabanni.

Wa’adin da Jam’iyyar APC ta ba kwamitin Mai Bala Buni zai kare a watan nan, har yanzu ba ayi zabe ba, kuma ba a sa ranar da za a san wadanda za su rike jam'iyyar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel