Sanata Rochas Okorocha ya fadawa Ibo gaskiya game da masu zugasu a kan a barka Najeriya

Sanata Rochas Okorocha ya fadawa Ibo gaskiya game da masu zugasu a kan a barka Najeriya

  • Rochas Okorocha ya ba mutanen Kabilarsa shawara su guji kiran a barke
  • Sanatan na Imo ya ce Ibo ne za su fi tafka asara idan dai Najeriya ta rabe
  • Tsohon Gwamnan yake cewa Ibo sun shiga ko ina, suna neman na abinci

A karshen makon nan ne tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha, ya yi magana game da kirayen-kirayen da ake yi na cewa a raba Najeriya.

Sanatan mai wakiltar yankin Imo ta yamma a majalisar dattawa ya gargadi mutanen kabilar Ibo da cewa su za su fi kowa shan wahala idan aka barka kasar nan.

Jaridar PM News ta ce jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana wannan ne yayin da yake zanta wa da wasu kungiyoyin mata a birnin tarayya watau Abuja.

KU KARANTA: APC ta doke PDP a zaben cike gurbi a Jihar Jigawa

Shawarar Rochas Okorocha

Sanata Rochas Okorocha ya shaida masu cewa abin da ya kamata ‘yan Kudu maso gabas su yi shi ne kokarin ganin yadda za a gyara Najeriya, ba a raba ta ba.

‘Dan majalisar yake cewa Ibo mutane ne da suka ratsa ko ina, don haka ya ba su shawarar su yi fatali da masu buga tambarin a raba kasa, kowa ya yi hanyarsa.

Herald ta rahoto Rochas Okorocha ya na cewa: “Mutumin Ibo ne kurum yake zuwa wuri, ya yi zamansa, ya saye fili, ya gina gida da iyalinsa, bai jin dar-dar.”

“Mutanen kabilar Ibo za su fi kowa asara idan Najeriya ta wargaje.” Inji Sanata Rochas Okorocha.

Sen. Rochas Okorocha
Sanatan Imo, Rochas Okorocha Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya tabo salsala, ya ce rabinsa Fulani, rabi Hausa, rabi Babarbare

“Mafi yawan shugabannin Najeriya da su ka yi nasara, sun hada dangataka da Ibo. Ko dai sun auri Ibo, ko suna da alaka da su. Zan iya kiran irinsu tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar, Janar Buba Marwa, ‘dan misali kadan kenan."

Ana kiran a raba Najeriya

Kungiyoyi irinsu Indigenous People of Biafra, IPOB, and the Movement for the Actualisation of Sovereignty State of Biafra, MASSOB suna neman a raba Najeriya.

A makon da ya gabata kun ji cewa kungiyoyin Arewa a karkashin tafiyar NCM sun yi taron-dangi, suna neman Nnamdi Kanu ya amsa laifin kashe ‘Yan Arewa a Kudu.

Northern Consensus Movement ta na rokon US, UK da EU su kawo Kanu ayi masa hukunci a gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel