Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniya

Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniya

  • Wata mahaifiya ta baiwa yaronta karami mamaki a ranar zagayowar haihuwarsa wanda jama'a suka saki baki suna kallo
  • Yaron mai shekaru 10 a duniya ya samu kyautar mota kirar BMW daga mahaifiyarsa kamar yadda wasu hotuna suka bayyana
  • Yayin da wasu jama'a suka dinga jinjinawa mahaifiyar yaron, sauran sun dinga tsokaci masu bada dariya kan kyautar

Mahaifiyar yaro mai shekaru 10 ta bashi matukar mamaki tare da birgeshi yayin da ya cika shekaru 10 a duniya.

Mahaifiyar 'yar asalin Najeriya wacce har yanzu ba a binciko sunanta ba ta baiwa yaronta kyautar mota kirar BMW cike da salo.

KU KARANTA: Hotunan daliban Kebbi da jami'an tsaro suka ceto daga wurin 'yan bindiga kwance a asibiti

Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniya
Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniya. Hoto daga @kingtundeednnut
Asali: Instagram

KU KARANTA: Tsoffin gwamnoni 6 a Najeriya dake fadi a ji har yanzu a siyasar jihohinsu

A wasu hotuna da wani mai suna @Kingtundeednut ya wallafa a Instagram, an ga yaron ya sanya kayan alfarma inda suka jeru cike da kauna tare da mahaifiyarsa da kanninsa.

A daya daga cikin hotunan, an ga yaron tsaye cike da murmushi da murna kuma rike da makullan motarsa.

Kafar sada zumunta ta yi martani kan gagarumar kyautar

Wasu mutane sun dinga mamakin inda yaro mai karancin shekaru haka zai je da mota yayin da wasu suka dinga addu'ar Ubangiji ya basu damar yi wa 'ya'yansu makamanciyar wannan gatan.

@bjwisky cewa yayi: ''Da fatan malaman makaranta a Najeriya ba zasu yi wa wannan yaron hassada ba."

@yemiwo_azaman martani tayi da cewa: "Toh wannan yaron yana da mota, sannan kuma a ce a kasar nan kada mu yi damfarar yanar gizo?"

@therealesthereduh_backup mamaki tayi tare da cewa: "Toh ina zai tuka ya je?"

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya ziyarci sojojin da suka samu raunika yayin yakar 'yan ta'adda kuma suke kwance a asibitin koyarwa na Maiduguri.

A wata takarda da aka fitar a Maiduguri ta hannun Kanal Ado Isa, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar Operation Hadin Kai kuma ya wallafa a Facebook, ya ce COAS ya je Maiduguri domin ziyarar kwanaki hudu don duba aiki da jin dadin dakarun dake jihar.

"A yayin ziyarar, ya tabbatarwa da dakarun cewa zasu samu kula sosai a bangaren lafiya tare da tallafi a yakin da suke da ta'addanci."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng