Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace

Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace

  • Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya dawo gida Najeriya kuma ya garzaya inda ya gana da iyayen daliban Tegina
  • Kamar yadda aka sani, wasu miyagun 'yan bindiga sun sace daliban makarantar Islamiyya a watan da ya gabata
  • Gwamnan ya jajantawa iyayen yaran inda ya kara da cewa zai tabbatar da karbo yaran daga hannun miyagun

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya samu ganawa da iyayen dalibai 136 na makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko dake Tegina, wadanda aka sace a watan da ya gabata.

Gwamnan ya shilla kasar waje bayan sa'o'i kadan da sace yaran, yayin da mataimakinsa ya dinga kokarin ganin an sakosu, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan dawowarsa kasar, Bello ya kaddamar da kungiyar sintiri ta musamman domin magance matsalar tsaro da ke cigaba da gawurta a jihar kuma ya karasa Tegina domin ganawa da iyayen yaran.

KU KARANTA: Tsoffin gwamnoni 6 a Najeriya dake fadi a ji har yanzu a siyasar jihohinsu

Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace
Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan COAS Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a Maiduguri

Bello ya gana da iyayen yaran tare da sauran masu ruwa da tsaki a fadar sarkin Kagara, Alhaji Ahmed Garba Gunna.

Ya jajanta musu tare da tabbatar musu da cewa gwamnatinsa na yin duk abinda ya dace wurin ceto yaran, Newswire ta ruwaito.

A farkon watan nan ne gwamnatin jihar tace ta fara sasanci da kungiyar 'yan bindigan da suka shirya sace yaran makarantan.

Gwamnatin ta ce ba wai bata san cinikin da aka fara tsakanin iyayen yaran da aka sace ba da masu garkuwa da mutanen ba, amma ta jaddada cewa ba za ta biya ko sisin kwabo ba domin ceto yaran.

A wani labari na daban, Alhaji Yusuf Galami, dan takarar jam'iyyar APC a zaben maye gurbi da aka yi domin cike kujerar majalisar tarayya ta mazabar Gwaram a jihar Jigawa ya samu nasara.

Farfesa Ahmad Shehu, baturen zaben, bayan tattara kuri'u daga akwatuna 248 ya bayyana Galambi a matsayin mai rinjaye da kuri'a 29,372 a kan Kamilu Inuwa na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 10,047.

"Bayan Galambi ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben maye gurbin, ya zama mai nasarar a zaben," Shehu ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Gwaram kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng