Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya

Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya

  • Wani sifetan dan sanda a jihar Enugu ya shiga hannun hukuma bayan yayi luguden wuta babu gaira, ba dalili
  • Harbin da dan sandan ya dinga ya janyo mutuwar mutum 5 inda wasu mutum 4 suka jigata kuma suke asibiti
  • Gwamnan jihar Enugu ya nuna tausayawarsa yayin ziyarar mutum 4 da yayi kuma ya sha alwashin daukar dawainiyarsu ta magani

Dan sanda mai mukamin sifeta a jihar Enugu ya shiga hannu bayan luguden wutan da yayi a ranar Lahadi wanda ya janyo mutuwar mutum biyar a take.

Mutum hudu kuwa sun samu miyagun raunika inda a halin yanzu suke karbar taimakon masana kiwon lafiya a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Enugu, The Cable ta ruwaito.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, hukumar 'yan sandan jihar ta ce har yanzu ba a san dalilin dan sandan na luguden wutan ba duk da wasu sun tabbatar da cewa giya ya sha yayi tatil.

KU KARANTA: Sojoji sun tare shanun sata 154, sun damke miyagu 44 a Zamfara

Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya
Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan daliban Kebbi da jami'an tsaro suka ceto daga wurin 'yan bindiga kwance a asibiti

"Mutum hudu sun jigata kuma suna samun kulawar likitoci. Mutum biyar da suka samu miyagun raunika sun riga mu gidan gaskiya kuma an mika gawawwakinsu ma'adanar gawa dake asibiti domin kara bincike," kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatar.

Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, wanda ya ziyarci wadanda lamarin ya ritsa dasu a asibitin koyarwa na jam'iar jihar Enugu, ya shiga matukar damuwa.

Kwamishinan yada labarai, Nnanyelugo Chidi Aroh, wanda yace gwamnan ya tausayawa wadanda lamarin ya faru dasu, yace yayi musu fatan samun sauki.

Ugwuanyi ya sanar da cewa zai dauka nauyin kudin maganin wadanda lamarin ya ritsa dasu.

Ya bar wasu kudade a hannun hukumar asibitin domin a fara aiki, The Nation ta ruwaito.

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya ziyarci sojojin da suka samu raunika yayin yakar 'yan ta'adda kuma suke kwance a asibitin koyarwa na Maiduguri.

A wata takarda da aka fitar a Maiduguri ta hannun Kanal Ado Isa, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar Operation Hadin Kai kuma ya wallafa a Facebook, ya ce COAS ya je Maiduguri domin ziyarar kwanaki hudu don duba aiki da jin dadin dakarun dake jihar.

"A yayin ziyarar, ya tabbatarwa da dakarun cewa zasu samu kula sosai a bangaren lafiya tare da tallafi a yakin da suke da ta'addanci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel